Bayan da kotun koli ta zartar da hukunci na tabbatar da nasarar Shugaban kasa, Bola Tinubu a zaben 2023, jam’iyyun adawa sun yi kunkurin shirya kawance domin tunkarar APC a 2027, sai dai kuma matsaloli sun turnuke wannan yukurin na jam’iyyun adawa.
Amma tambayoyin mai muhimmanci da mutane ke ci gaba da yi ita ce, yadda jam’iyyun adawan za su samu nasarar yin wannan kwance bayan da sun gaza magance matsaloli da yawa kan lamarin.
- Kungiyar Lauyoyi Ta Tabbatar Da Fara Gurfanar Da Masu Laifukan Zaben 2023
- Gwamnan Zamfara Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Garin Mada
Jiga-jigan ‘yan siyasa a tsakanin jam’iyyun adawa sun ci gaba da tattaunawa tare da shawartar juna kan kafa kwancen siyasa ta yadda za su sami karfin tunkarar Shugaba Tinubu wanda zai nemi wa’adin mulki na biyu bayan shudewar mulkinsa na farko a 2027.
Idan za a iya tunawa dai, an samu irin wannan kwancen siyasa a 2013 lokacin da jam’iyyun CPC, ACN, ANPP, APGA da kuma wani bangare na jam’iyyar PDP suka dunkule wuri daya tare da samar da jam’iyya daya mai suna APC.
Tun a ranar 15 ga Oktoban 2023, dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP a 2023, Atiku Abubakar ya yi kira ga daukacin jam’iyyun adawa da ke kasar nan wajen samar da kwancen siyasa domin takatar da APC na yunkurin mayar da Nijeriya karkashin jam’iyya daya. Ya dai bayyana hakan ne lokacin da yake amsar bakwancin mambobin kwamitin zartarwa na cibiyar hadakar jam’iyyu.
Ya ce, “Muna ganin yadda jam’iyyar APC tane kara kaimi wajen mayar da Nijeriya tsarin jam’iyya daya. Idan har muka kasa hada kai wajen kalubantar jam’iyya mai mulki, za ta lalata mana dimokuradiyya kuma hakan zai shafi goben yaran da za a haifa nan gaba.”
Bayan haka, jam’iyyun PDP, NNPP, ADC, APM, SDP, YPP, da ZLP sun kafa wata kungiya da suka kira da CCPP bayan ganawa da shugabannin jam’iyyun guda 7 da ya gudana a shalkwatan jam’iyyar SDP da ke Abuja a ranar 6 ga Disambar 2023.
Shugabannin jam’iyyun adawa na ci gaba da sokar gwamnatin Tinubu na cewa ya kawo wasu tsare-tsaren tattalin arziki da suka janyo tsadar rayuwa da fatara da kuma radadin kuncin rayuwa ga ‘yan Nijeriya. Haka kuma sun bayyana damuwarsu kan karuwar rashin tsaro a kasar nan.
Sai dai kuma sakataren jam’iyyar APC na kasa, Felid Morka, ya bukaci ‘yan Nijeriya kar su dauki kawacen jam’iyyun adawa da muhimmanci, su kaance da jam’iyyar APC.
Bincike ya tabbatar da cewa har yanzu ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyya daban-daban da masu ruwa da tsaki na jam’iyyun adawa ba su kammala amincewa da wannan kawancin ba tare da kin yin watsi da akidar jam’iyyunsu. Haka kuma ba su yarda da yi wa wata sabuwar jam’iyya rajista ba.
An bayyana cewa kafin kawancen jam’iyyun adawan ya yuwu, sai dukkan jam’iyyun sun bayar da takardunsu ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kafin su samu damar yi wa sabon jam’iyya rajista.
Ana ganin cewa wannan kawancen na jam’iyyun adawa zai yi wuya saboda akwai bambance-bambancin ra’ayoyi a tsakanin mambobin jam’iyyun.
Masu bincike sun bayana cewa matsalolin da ke barazana ga dorewar kawancen dai sun hada da rikicin cikin gina da rabuwar kai a tsakanin manyan jam’iyyun adawa. Sun kuma bayyana cewa za a samu matsala wajen fitar da dan takara idan har aka samu nasarar yin wannan kawance.
Haka kuma suna ganin cewa wasu manyan ‘yan siyasa masu matukar karfi da ke cikin gwamnatin Tinubu ba za su taba bari wannan kawanci ya samu nasara ba, domin kalubalantarsa a 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp