Sanata Adams Oshiomhole ya roki ‘yan Nijeriya da su yi hakuri da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya kai kashi 34.19 a watan Yuni 2024, a cewar Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS).
- An Kama Wanda Ya Kitsa Kashe Janar Udokwere A Kano
- Sarkin Katsina Ya Jinjinawa Tinubu Kan Aikin Titin Maraba Zuwa Katsina
Wannan ya faru ne saboda sabon tsarin musayar Naira da kuma cire tallafin fetur, wanda ya sa farashin kayayyaki ya yi tsada sosai.
Oshiomhole, wanda ke wakiltar Edo ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya yi imanin cewa manufofin Tinubu za su yi nasara daga bisani, inda ya roki ‘yan Nijeriya su kara hakuri.
“Wadannan manufofi na bukatar fiye da shekara guda kafin sakamako ya bayyana,” in ji Oshiomhole a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels.
“Me zai amfanar da shugaban kasa idan ya zabi manufofi da ba za su kawo jin dadi a nan gaba ba?”
“Saboda haka, yana da muhimmanci mu yi imani cewa abubuwa za su yi kyau a nan gaba,” in ji shi.