Hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta bayyana cewa dole jam’iyyun ƙasar da aka yi wa rajista su bayyana inda suka samu kuɗin kamfe ɗinsu da kuma bin ƙa’idojin da aka gindaya na kashe kuɗi a lokacin yaƙin neman zaɓe.
BBC ta rawaito cewa, Shugaban na INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a yayin wata hira da gidan talabijin na Trust TV a Nijeriya inda ya ce akwai kuma adadin da aka ƙayyade na irin gudunmawar kuɗi da mutum zai iya bai wa jam’iyya a yaƙin neman zaɓe.
- 2023: Ko INEC Za Ta Iya Gudanar Da Sahihin Zabe?
- 2023: Sarkin Kano Da Kungiyoyin Fararen Hula Sun Bukaci INEC Ta Gudanar Da Sahihin Zabe
Haka kuma ya ƙara jaddada cewa jam’iyyu ba za su iya karɓar tallafin kuɗi ba daga ƙasashen waje.
A cewarsa, idan ma an samu irin wannan tallafin, ya zama dole a tura wa hukumar zabe waɗannan kuɗaɗe.