Shugaban Hukumar Kula Da Shige Da Fice ta Ƙasa (NIS), Idris Isah Jere ya bayyana cewa ƙaddamar da ofishin fasfo na Ilesa da ke Jihar Legas zai ƙara saukaka samar da fasfo ga ‘Yan Nijeriya.
A jawabin da ya gabatar a wurin ƙaddamarwar, CGI Idris Isah Jere ya bayyana cewa, “Ina farin ciki da rana irin ta yau – Talata 28 ga watan Maris da muka zo wannan gari na Ilesa don kaddamar da cibiyar yin Fasfo na zamani.
“A farkon shigarmu wannan ofis na shugabancin hukumar NIS, na bayyana karara cewa NIS karkashin kulawata za ta yi kokarin samar da ingantattun tsaruka da ayyuka ga al’ummarmu kasa. Na bayyana fannoni Uku da zan fi mayar da hankali kansu, wadanda suka hada da kaddamar da cibiyoyin fasfo na zamani, kula da kan iyaka da walwalar jami’anmu.”
Har ila yau, ya ƙara da cewa, Hukumar NIS ta himmatu wajen samar da ayyuka da tsaruka da zai dace da bukatun al’ummarmu tare da yin amfani da kayan ayyukanmu ta yadda suka fi cancanta. Gudanar da ingataccen fasfo na zamani (e-Passport) yana da mahimmanci sosai ga yunkurinmu na isar da ayyukan hukumarmu ta yadda yafi dacewa ga ‘yan kasarmu.
“Ina da yakinin cewa, samar da wannan cibiya zata rage jinkirin da ake samu wajen yin fasfo. Don haka ina ba masu bukatar samun fasfo da su bi ka’idodin da aka gindaya don gudanar da fasfo din cikin sauki da walwala, su tura bukatar mallakar fasfo din a manhajar Intanet, su biya kudi ta (https://www.passport.immigration.gov.ng) tare da tabbatar da cewa bayanan fasfo dinsu ya yi daidai da wanda ke kan bayanan katin shaidar zama dan kasa (NIN) din su don guje wa jinkiri sabida rashin daidaituwa na bayanan.
“A yau, Ilesa ta shiga sahun manyan cibiyoyin yin fasfo na duniya kamar kasashen Kanada, Burtaniya da Amurka wadanda suka yi nasarar komawa bangaren ingantaccen tsarin fasfo na zamani (e-Passport)”. Ya bayyana