Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin hako mai na farko a jihar Nasarawa a daidai lokacin da Nijeriya ke shirin ninka adadin danyen man da take hakowa kullum daga ganga miliyan 1.7 zuwa ganga miliyan uku a kowace rana.
Haka kuma kasar na fatan kara yawan man da take tara wa daka ganga biliyan 37.8 zuwa ganga biliyan 50 nan da shekaru 10 masu zuwa.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da aikin da kamfanin Spud-in zai jagoranta na rijiyar mai Ebenyi-A da ke karamar hukumar Obi ta jihar Nasarawa, shugaba Buhari ya ce gwamnati ta kuduri aniyar bunkasa yadda ake hako mai a Nijeriya ta hanyar zama a gababa a kasuwannin duniya.
Talla