Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta himmatu wajen yin amfani da karfin fasahar zamani wajen bunkasa tattalin arziki, inganta harkokin mulki da inganta rayuwar al’ummar jihar baki daya.
Gwamna Sani, wanda ya bayyana hakan a lokacin da ya ke kaddamar da bude taron koli na baje kolin fasahar zamani ta mutum-mutumi (AI Robotics) karo na uku wanda kungiyar masana Kwamfuta ta Nijeriya, NCS ta shirya gudanarwa a Kaduna, ya ce, da ci gaban fasahar mutum-mutumi, “Gwamnatin Kaduna ba za ta bari a bar ‘yan jiharta a baya ba”.
- An Kama ‘Yan Sintiri 10 Kan Zargin Kashe Limamin Garin Mada
- Majalisar Dokokin Edo Na Shirin Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar
Gwamnan, wanda ya samu wakilcin mataimakiyarsa, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta bayyana cewa, al’ummomin da suka yi watsi da fasahar kere-kere ta zamani (AI Robotics) za a bar su a baya saboda “(AI Robotics) sun zama wani jirgin ruwan tsira da dole sai an shiga in ana neman tsira,” in ji ta.
Dakta Hadiza Balarabe Sabuwa, ta kuma yabawa NCS bisa lambar yabo da ta bai wa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani a matsayin Gwarzon Gwamna kan fasahar zamani ta Nijeriya ta 2023 da aka gudanar a jihar Legas.
Shima da yake nasa jawabin, shugaban NCS a kasa, Dr. Muhammad Sirajo Aliyu, ya godewa gwamna Uba Sani na jihar Kaduna da ya karbi bakuncin taron, da kuma tallafin da Gwamnan ya bai wa Kungiyar.