Kamfanin rarraba Wutar Lantarki ta Kaduna, KAEDCO, ya amince ya maido da wutar lantarki a cikin Birnin Kebbi cikin wasu sa’o’i kadan nan gaba.
Hakan ya biyo bayan sa baki da Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yi na sasanta rikicin da ke tsakanin kamfanin da Sojojin Nijeriya.
Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Babale Umar Yauri ne ya sanar da hakan bayan wata ganawa da mahukuntan KAEDCO da shugabannin rundunar sojin da sauran shugabannin hukumomin tsaro a ofishinsa da ke Birnin Kebbi.
Gwamnan ya umarci SSG da a samar da zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu da ke rikici da juna wanda zai share fagen maido da wutar lantarki ga mazauna babban birnin jihar.
Da yake zantawa da manema labarai bayan kammala taron, Babale Umar Yauri a madadin gwamnatin jihar Kebbi ya nemi afuwar hukumar ta KAEDCO a kan abin da ya samu ma’aikatansu, tare da yin Allah wadai da irin halin da suke ciki, yana mai ba da tabbacin gwamnati da jami’an tsaro za su samar da ingantaccen tsaro ga ma’aikatan kamfanin don gudanar da ayyukansu a cikin jihar.
Hakazalika SSG ya jaddada cewa kwamandan rundunar a Birnin Kebbi bai baiwa wani soja izinin rike ma’aikatan KAEDCO ba ballantana ya goyi bayan abin da ya faru, domin sojoji ba sa amince wa da ayyukan rashin bin doka da oda ba.
Sakataren gwamnati ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bin doka da oda, inda ya ce duk ma’aikacin KAEDCO da aka samu yana gudanar da ayyukansa ba bisa ka’ida ba a kai rahoto ga mahukuntan kamfanin domin daukar matakin ladabtarwa.
Ya bayyana karara cewa Gwamna Abubakar Atiku Bagudu zai ci gaba da ba da tallafin kayan aiki ga KAEDCO don tabbatar da samar da wutar lantarki akai-akai a duk sassan jihar Kebbi.
Haka Kuma ya godewa jami’an KAEDCO bisa yadda suka magance rikicin tare da nuna jin dadinsu ga jami’an soji da suka shawo kan lamarin cikin gaggawa.
A nasa jawabin, shugaban yankin KAEDCO mai kula da jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara, Mista Sunday Yahaya, ya yaba da fatan alheri da hakuri da gwamnatin jihar Kebbi ta yi kan wannan mummunan lamari.
Mista Sunday Yahaya ya kuma ba da hakuri cewa lamarin ya koma ga wannan matakin, amma ya yi kira ga jama’a da su ba ma’aikatan kamfanin hadin kai wajen gudanar da ayyukansu.
Shugaban yankin na KAEDCO yayin da ya umarci dukkan ma’aikatansu da su koma bakin aiki cikin gaggawa, ya shawarci masu amfani da wutar lantarki da su kai rahoton ma’aikatan KAEDCO da suka yi kura-kurai ga hukumomin da suka dace, inda ya tabbatar da cewa kamfanin yana da tsarin ladabtar da ma’aikatansa.
Taron wanda SSG ya jagoranta ya samu halartar mukaddashin shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Safiyanu Garba Bena da wakilin kwamishinan ‘yan sanda, kwamandan rundunar sojojin na Birnin Kebbi, Kwamandan Bataliya Light Tank Battalion 223, Zuru, Wakilin Kwanturolan Kwastam, da Ma’aikatan Gudanarwa na KAEDCO.
A karshen taron bangarorin uku da aka yi tsakanin gwamnatin jihar da shugaban hukumar KAEDCO da wasu zababbun hukumomin tsaro, an rattaba hannu kan wani kudiri da dukkanin bangarorin da abin ya shafa suka sanya hannu.