A cikin wani gagarumin sauyin da Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ta samar shi ne gina ma’aikatun sarrafa ridi a sassa hudu da ke jihar, matakin da babban jigo ne ga ci gaba a fannin harkokin noma tare da bunkasa tattalin arzikin jihar.
Wannan mataki na Gwamnatin Buni ya na daya daga cikin hanyoyi mafi sauki da nagarta wajen farfado da ci gaba tare da bunkasa harkokin tattalin arziki, na kokarin alkinta albarkatun da al’ummar jihar Yobe suke dashi na gida. Saboda babban al’amarin da talaka a Yobe yake alfahari dashi shi ne noma; kuma a matsayinsa na muhimmiyar damar da yake da iko da ita a hannunsa kuma wadda rayuwarsa ta yau da kullum ta ta’allaka da shi.
- Jihohi 11 Sun Kammala Jigilar Dawo Da AlhazansuÂ
- Ko Dakatar Da Harajin Shigo Da Abinci Zai Yi Tasiri?
Ana ganin babu wani abu da zai taimaki talaka kamar samar masa da cibiyar da za ta alkinta abin da yake nomawa, tare da bunkasa shi.
Gwamna Buni na da kyakkyawar fatan ganin ya dora jihar Yobe bisa kyakkyawan turbar da za ta kai ga bunkasa harkokin noma tare da zamanantar dashi, daidai yake da kawo dauki ga daukacin rayuwar al’ummar jihar, saboda shi kadai ne bangaren da kyautatuwar sa ya shafi kowane ci gaba musamman halin da ake fuskanta sakamakon rikicin Boko Haram da jihar ta sha fama dashi.
Ayyukan wadannan cibiyoyin sarrafa amfanin gona mafi kima a kasuwar duniya da musayar kudade tsakanin Nijeriya da kasashen da take huldar cinikayya, wadanda ana matakin kammala su a Machina, Nguru, Potiskum da Damaturu dake jihar. Wannan babbar dabara ce shiga rijiya da dawo (fura) kasancewar jihar Yobe na daya daga cikin jihohin Nijeriya wadanda suke gamsar da kasuwannin duniya da ridin da suke nomawa; mai yawan gaske tare da inganci. Kuma samar da wadannan masana’antu zai bai wa gwamnatin jihar Yobe damar jifar tsuntsu biyu da dutsi daya; samar da ayyukan yi ga matasa, bunkasa tattalin arziki da gagarumin sauyi a harkokin noma daidai da zamani. Sannan uwa uba kuma, samar wa jihar kudin shiga ta fannin hulda da kamfanonin manyan kasashen duniya tare da zuwan masu zuba jari a harkar noman ridi.
Baya ga farfado da fannin noma da harkokin ilimi, Gwamna Buni ya kafa manyan kwamitocin tuntuba na kwararru kan yadda zai kawo gagarumin sauyi a bangarorin saboda babu al’ummar da za ta ci gaba ba tare da harkokin noma da ilimi ba. Sannan a halin da ake ciki yanzu, akwai bukatar karkatar da tunanin jama’a zuwa ga abubuwan da za su sanya rage dogaro ga gwamnati tare da samar da abubuwan yi domin dogaro da kai.
Masana’antun sarrafa ridi a jihar Yobe kyakkyawar shimfida ce kuma tanadi ne mai gwabi da gudana nan da shekaru masu yawa, nan gaba, kuma ko shakka babu al’umma masu tasowa za su ci moriyarsa fiye da yanzu tare da godiya dangane da kyakkyawan shirin da Gwamnatin Gwamna Buni ta yi wa rayuwar su. Kuma ta sakamakon hakan, sauran jihohin Nijeriya za su biyo sahun Gwamna Buni dangane da wannan hangen nesa, saboda lokaci ya yi da ya dace gwamnatoci su samar da wata madafa bayan albarkatun mai, kuma mai dorewa don samun madogara a tsarin gudanar da harkokin tattalin arziki. Har wala yau, Nijeriya ta na fuskantar matsaloli da kalubale daban-daban dangane da makomar matasa.
Yobe jiha ce da Allah ya azurta da filayen noman rani da damina. Bincike ya tabbatar da cewa, noma, kiwo da kamun kifi kadai idan an bunkasa su, za su rike kaso mai yawa na sha’anin gudanarwar yau da kullum.
Gwamna Mai Mala Buni ya yi zurfin tunani tare da yin la’akari da dimbin alfanun da harkokin noman ridi suke dashi, matsayinsa na nau’in amfanin gona wanda yake da matukar kima a hada-hadar kasuwanci ta duniya.
Wani rahoton binciken da Hukumar kula da Abinci da Harkokin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta gudanar, ya bayyana Nijeriya a matsayin ta shidda (6) wajen fitar da ridi zuwa Kasashen waje a 2021, kuma na biyu daga cikin kayan amfanin gona da ake fita da su kasuwannin hada-hada na duniya bayan Koko. Rahoton ya kara da cewa, baya ga sarrafa ridi zuwa man girki, wasu kamfanoni da masana’antu suna alkinta ridi zuwa kayan abinci daban-daban, magunguna da makamantan su.
A hannu guda kuma, Nijeriya tana samun makudan kudin shiga ta hanyar fitar da ridin, wanda kimanin kaso 90 cikin dari na ridin da ake fita dashi daga Nijeriya ana kai shi China da Japan. Kamar yadda Shugaban kungiyar manoma ridi ta Nijeriya, Sheriff Balogun ya bayyana, tare da karin hasken cewa kowace shekara Nijeriya tana samun kudin shiga na kowane ton daya kan Dala 700 zuwa Dala 1400, ta hanyar fitar da ridi zuwa waje. Inda binciken ya ci gaba da cewa, a kebance akwai huldar kasuwanci tsakanin Tarayyar Nijeriya da Japan, wanda ya kai ga fitar da ridi na kimanin Dala biliyan daya a 2022.
Allah ya albarkaci jihar Yobe da maka-makan filayen noman da za a iya noma dubban hektoci (kadada) na ridi, wanda baya ga Kasashen da na ambata a baya, akwai karin wasu da ke ribibinsa, wadanda sun hada da Turkiya, Indiya, Bietnam, Netherlands, Jamus, Girka, Faranse, Poland, da makamantan su. Wannan wani sabon shafi ne na samar da sabuwar Yobe tare da samar da dubun-dubatar ayyukan yi da dogaro da kai.
Jihohin da ke kan gaba wajen noma ridi su ne: Jigawa, Nasarawa, Benuwe, da Sokoto; sauran sun hada da jihohin Yobe, Katsina, Gombe, Kogi, da Plateau. Yayin da masana suka nuna cewa, Nijeriya tana fitar da kimanin ton 500,000 na ridi mafi kima da daraja zuwa kasuwar duniya da cinikayyar kimanin Dallar Amurka Biliyan Daya a 2022.
Bincike ya tabbatar da cewa jihar Yobe tana da fadin murabba’in kilomita 47,153, kana da adadin mutanen da yawan su bai kai miliyan 4 ba, sannan sama da kaso 70 cikin dari na adadin filayen da Yobe take dashi bai wuce ana amfani da kaso 25 cikin dari ba. Amma a halin da ake ciki, Gwamnatin Gwamna Buni ta dauko hanyar sanyawa al’umma kaimin karkata akalar su zuwa noman damina da rani.
Idan mun kwatamta da jihar Kano, mai adadin filin murabba’in kilomita 20,131 sai kuma jihar Katsina mai murabba’in kilomita 23,938, wanda idan ka hada su baki daya, kadan suka zarta jihar Yobe. A hannu guda kuma suna da yawan al’umma kimanin mutum miliyan 35, wanda hakan yake nuni cewa sun ninka jihar Yobe sau 6.
Bugu da kari, su dukan; Kano da Katsina, ci gaban su ya dogara ne kan harkokin noma- a matsayin babbar hanyar da suke samun kudin shiga, sannan da la’akari da jihar Kano a matsayin jiha mafi bunkasar tattalin arziki a Arewacin Nijeriya.
Lokaci ya yi wanda al’ummar jihar Yobe za ta zage damtse domin cin gajiyar wadannan alkhairar da gwamnatin Hon. Mai Mala Buni ke kawowa.
Gwamna Buni ya yi wa al’ummar jihar Yobe tare da manyan manoman jihar babban albishir cewa daga yanzu ba su ba wata fargabar rashin samun ciniki domin tuni wasu manyan kamfanonin kasashen Turai da Gabas-ta-tsakiya suka nuna sha’awarsu ta fara huldar kasuwancin ridi da jihar Yobe, musamman yadda faduwa ta zo daidai da zama, sakamakon yadda jihar ta mallaki Filin Jirgin Dakon Kaya.
Gwamnatin Gwamna Buni ta yi kokari sosai ta fuskar farfado da harkokin tattalin arziki da kasuwanci a jihar Yobe, wanda baya ga wadannan masana’antu na sarrafa ridi, gwamnatin ta gina kasuwannin zamani a manyan garuruwan jihar; a birnin Damaturu, Gashuwa, Potiskum, Nguru da Gaidam.