Manyan malaman addinin Musulunci na Arewa da wasu ‘yan majalisar tarayya sun bayyana damuwarsu kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a kasa tare da yadda ake amfani da kafafen sada zumunta ta hanyar da ka iya jefa kasa cikin rudani idan ba a dauki mataki ba.
Wannan kira ya fito ne yayin taro da majalisar Koli ta shari’ar musulunci ta shiryawa malaman addinin musulunci dake Arewacin Nijeriya wanda aka gudanar a Kaduna, inda Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, tare da wasu sanannun sanatoci da malamai suka bukaci a dauki matakan hadin gwiwa domin daidaita harkokin kafafen sada zumunta da kuma karfafa hadin kai tsakanin Musulmai.
- Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc
- Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya
A nasa jawabin, Sanata Abdulaziz Yari da Jagoran Majalisar Wakilai, Honarabul Alhassan Ado Doguwa, sun jaddada cewa rashin tsaro da amfani da kafafen sada zumunta suna da alaka mai karfi, suna kuma bukatar shugabanci mai hangen nesa da hadin kai.
Yari ya bayyana cewa, matsalar tsaro a Arewa ta samo asali ne daga yadda ake amfani da albarkatun kasa da ke yankin ta hanyar da ba ta dace ba, yana kuma gargadin cewa bai kamata a dora laifi kawai a kan gwamnati ba.
“Kafafen sada zumunta suna shafar kowa mai kudi da talaka. Dole ne a tsara dokoki masu tsauri domin kare al’umma,” in ji shi
Sanata Yari ya jaddada cewa giɓin tattalin arziki tsakanin Arewa da Kudu yana kara faɗaɗa, don haka ya buƙaci al’ummar Arewa da su rungumi aikin yi, kirkire-kirkire da dogaro da kai, maimakon dogaro da taimako daga waje.
Doguwa kuwa ya kara da cewa Majalisar Tarayya tana shirye ta tallafa wa duk wani mataki da zai karfafa hadin kai da kuma inganta dabi’un Musulunci.
Shima Sheikh Ahmad Gumi ya ce wasu kasashe na waje na amfani da rashin tsaro a Arewa ta hanyar yaudarar makiyaya marasa ilimi da tayar da fitina domin samun damar mallakar albarkatun kasa.
Ya bukaci a kara tattaunawa tsakanin mazhabobin Musulunci tare da aiwatar da sauye-sauye da za su daidaita tsakanin dokokin amfani da kafafen sada zumunta da kuma kare ‘yancin fadin albarkacin baki.
Taron ya kammala da yin kiran hadin kai da tattaunawa tsakanin mazhabobi, da kuma karfafa tattalin arziki.