Abokai, kasashen yamma na da karfi matuka a fannin yada labarai a duniya, muna kallo da kuma sauraron rahotannin da kafofin yada labarai karkashin jagorancinsu ke watsawa. Amma ko kun taba nuna shakku kan gaskiyarsu?
A matsayin jarumai masu tsage gasiya, aikin ‘yan jarida shi ne kokarin gano abubuwa tare da fadawa duniya gaskiyar lamari. Amma, abin takaici shi ne, kwanan baya wani masanin Turai mai suna Jan Oberg ya fayyace cewa, a shekarun baya, majalisar dokokin kasar Amurka ta zartas da wani kudiri inda aka ware kudi har dallar Amurka biliyan 1.5, don horas da ‘yan jaridar kasashen yamma cikin tsawon shekaru 5, don su rubuta labaran shafawa kasar Sin bakin fenti. A hakika, wannan ba shi ne na farko da ta yi haka ba, a lokacin yakin cacar baka ma, hukumar leken asirin Amurka ta CIA ta gudanar da wani shiri mai suna “Operation Mockingbird”, inda suka sayi ‘yan jarida a kalla 400 da manyan kafofin yada labarai 25.
‘Yan siyasar Amurka sun biya ‘yan jarida don kirkirar labaran zamba, da nufin gurbata gaskiya. Wannan mataki ya zubar da mutuncin aikin jarida da na Amurka, kuma labaran da suka kirkira babu gaskiya a cikinsu. (Mai zane da rubutu: MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp