• English
  • Business News
Friday, October 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kai Karar Gwamnatin Japan Gaban Kotu Da Al’ummar Kasar Suka Yi Saboda Zubar Da Ruwan Dagwalon Nukilya A Cikin Teku Mafari Ne Kawai

by CMG Hausa
2 years ago
Japan

Jiya Jumma’a 8 ga watan Satumba, al’ummar kasar Japan sama da dari sun gabatar da kara ga wata kotun dake yankin Fukushima na kasar Japan, inda suka zargi gwamnatin kasar gami da kamfanin samar da wutar lantarki na Tokyo wato Tokyo Electric Power Company a turance, da aikata laifin zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku ba bisa doka ba, tare da bukatar kotun da ta yanke musu hukuncin dakatar da wannan danyen aiki, abun da ya kasance kara ta farko da aka gabatar dangane da bukatar dakatar da zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku a kasar Japan, kana, kokari ne na daban da jama’ar kasar suka yi na kare hakkokinsu bisa doka, bayan da wasu kungiyoyin al’umma suka gabatar da kara kan firaministan kasar, Fumio Kishida.

Takardar kai karar ta ce, kafin ta fara zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku, gwamnatin Japan ba ta taba gudanar da bincike a fannonin gurbata muhalli ko illoli ga muhallin halittu ba, kana, kamfanin samar da wutar lantarki na Tokyo na iya kara kafa manyan tankunan ajiye ruwan dagwalon nukiliyar maimakon zubarwa a cikin teku.

Don haka, al’ummar Japan na ganin cewa, gwamnatin kasar gami da kamfanin samar da wutar lantarki na Tokyo sun aikata laifin gurbata muhalli, da keta hakkokinsu a fannin kamun kifi da tafiyar da rayuwa cikin kwanciyar hankali, abu ne da ya keta doka.

Zubar da ruwan dagwalon nukiliya a cikin teku da gwamnatin kasar Japan take yi, babbar kasada ce da ba a taba ganin irinta ba a tarihi, wanda ke da alakar kut da kut da tsabtar muhallin yankunan teku a duniya, da lafiyar dan Adam gami da muradun zuriyoyinmu dake tafe.

Kai karar gwamnati da al’ummar Japan suka yi, ya shaida babbar damuwa daga bangarori daban-daban gami da Allah wadai da suka yi. Kwararru na ganin cewa, abun da wadannan mutanen Japan suka yi, zai iya kara karfafa gwiwar sauran mutane don su kiyaye hakkokinsu bisa doka ta hanyoyi daban-daban. (Murtala Zhang)

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa
Daga Birnin Sin

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

October 10, 2025
An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal
Daga Birnin Sin

An Jinjinawa Tallafin Kamfanonin Sin Ga Tsarin Bunkasa Masana’antun Senegal

October 9, 2025
Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025
Daga Birnin Sin

Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025

October 9, 2025
Next Post
Rashin Tausayi ‘Ina Fama Da Talauci, ‘Yan’uwana Masu Hali Sun Ki Taimako Na’

Rashin Tausayi ‘Ina Fama Da Talauci, ‘Yan’uwana Masu Hali Sun Ki Taimako Na’

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

Xi Ya Taya Kim Jong Un Murnar Cikar Jam’iyyar WPK Shekaru 80 Da Kafuwa

October 10, 2025
An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi 

October 10, 2025
Nijeriya

Haramcin Haƙar Ma’adanai: Majalisa Za Ta Kawo Ƙarshen Asarar Dala Biliyan 9 Duk Shekara

October 10, 2025
Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano

October 10, 2025
Yadda Rashin Isassun Malaman Turanci Da Lissafi Ke Shafar Ingancin Ilimi A Nijeriya (3)

Yadda Za A Magance Yawaitar Malaman Da Ba Su Cancanta Ba A Nijeriya – TRCN

October 10, 2025
Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

Gwamnatin Katsina Ta Rufe Makarantu 32 Masu Zaman Kansu Da Ba Su Da Lasisi

October 10, 2025
Japan

Burin ‘Yan Nijeriya Bai Cika Ba Tun Bayan Samun ‘Yancin Kai

October 10, 2025
Matatar dangote

ACF Ta Yi Zargin Shiri Na Musamman Don Rusa Matatar Man Dangote

October 10, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

October 10, 2025
Gwamnatin Kogi Ta Yaba Wa Tinubu Kan Naɗin Amupitan Shugaban INEC

Gwamnatin Kogi Ta Yaba Wa Tinubu Kan Naɗin Amupitan Shugaban INEC

October 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.