Hukumar ‘yansanda ta jihar Kano ta kama wani matashi mai shekaru 25, Mansur Umar, bisa zargin kashe saurayin ‘yar uwarsa a kauyen Kunya da ke karamar hukumar Minjibir.
Kakakin ‘yansandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da karfe 9:30 na dare ranar Juma’a, 9 ga Mayu, 2025. Wanda aka kashe, Sulaiman Musa, shi ma mai shekara 25, yayin ziyartar budurwarsa, Fiddausi Umar, a gidansa.
- Kantoma Na Ƙaramar Hukumar Shira Ya Rasu Kwanaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi
- NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC
A lokacin ziyarar, an yi zargin cewa dan uwan Fiddausi, Mansur Umar, ya radawa Sulaiman sanda a kai, inda ya yi masa mummunan rauni. An fara kai shi asibitin Kunya, daga nan kuma aka tura shi asibitin Murtala Muhammad na Kano, inda ya rasu da karfe 12:50 na safe ranar Asabar.
‘Yansanda sun ce sun tsare wanda ake zargi, kuma sashin binciken kisan kai ne ke gudanar da binciken.
Kwamishinan ‘yansanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yi Allah wadai da lamarin, yana kira ga zaman lafiya da kuma amfani da hanyoyin sulhu idan an samu rashin fahimta. Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da ba da rahoton duk wani abu da suke shakka don tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp