Wani babban Soja wanda ke aiki a ƙarƙashin shelƙwatar Brigade 14 a jihar Abia, ya yi wa kansa mummunar kisan gilla a ƙofar barikin Forward Operation Base (FOB) da ke babbar makarantar Ngwa, Abayi, a ƙaramar hukumar Osisioma.
Lamarin da ya jefa Sojojin cikin firgici, domin ba a samu takardar wasiyyar kashe kansa ba, kuma har yanzu ba a san dalilan da suka sa ya yanke shawarar ba kashe kansa ba. Vitalis, ɗan asalin Okpuala ne a Ngor-Okpuala, jihar Imo, ya ɓace tsawon makonni biyu kafin ya sake bayyana ya kashe rayuwarsa.
- Gwamnan Gombe Ya Gwangwaje Shugabannin Kananan Hukumomi Da Motoci
- Kwankwaso Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yin Katsa-landan A Harkokin Kano
Majiyoyi daga cikin hukumomin tsaro sun jaddada buƙatar yin bincike mai zurfi don gano musabbabin kisan kan, tare da yin taka tsan-tsan a kan yanke hukunci da wuri.
Sun yi nuni da cewa, ba a taba samun rahoton rikicin cikin gida ko ladabtarwar da aka yi wa sojan daga Bataliya ko shelƙwatar Birged ta 14 ba.
Abokansa aiki da hukumomin Soji ba su samu damar tuntubar sa ba a lokacin da ya bace, lamarin da ya kara dagula al’amura.
Vitalis ya kusa yin ritaya, wanda aka shirya a watan Oktoba, hakan ya daɗa ba abokan aikinsa mamaki game da shawarar da ya yanke na kawo karshen rayuwarsa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar (APRO), Laftanar Prince Innocent Omale, yace har yanzu bai amsa kira ko sakonnin neman tsokaci kan lamarin ba.