• English
  • Business News
Friday, October 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin: Amurka Ce Sanadin Matsalolin Abinci A Duniya

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Zhao Lijian, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya bayyana a wajen taron manema labarai da ya gudana a yau Litinin cewa, kasar Amurka ce ta haifar da dukkan matsalolin abinci da duniya ta fuskanta a lokutan baya.

A yanayin da ake ciki a halin yanzu, ya kamata al’ummun kasa da kasa su yi aiki tare, wajen tabbatar da zaman lafiya, da shirya tattaunawa, da samar da kyakkyawan yanayin da zai taimaka wajen warware matsalolin abinci da duniyar ke fuskanta. Ruruta wuta, da sanya takunkumai ba tare da kakkautawa ba, hakan ba zai taimaka wajen daidaita yanayin da ake ciki a shiyya ba, sai dai ma ya kara ta’azzara matsalar abincin da ake fama da ita.

A baya bayan nan, shugaban kasar Senegal, kana shugaban karba-karba na kungiyar tarayyar Afrika AU, ya ce takunkuman da kasashen yammacin duniya ke kakabawa Rasha sun yi matukar shafar yanayin samar da abinci a Afrika. Shirin samar da abinci na MDD a kwanan nan yayi gargadin cewa, mai yiwuwa ne bil adama ya fuskanci matsalar karancin abinci mafi muni da ba a taba gani ba tun bayan yakin duniya na II.

A yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai dangane da wannan, Zhao Lijian ya bayyana cewa, “A hakika dai, kasar Amurka ce sanadin matsalolin abincin da duniya ta fuskanta a lokutan baya.

Kasar Amurka da wasu tsirarrun kasashe suke rike tsarin cinikayyar abinci ta duniya, sun kafa wani tsarin ‘babakere a fannin abinci’, sun lahanta yanayin farashin abinci a kasa da kasa, kuma suna cigaba da samun kazamar riba ta hanyar tsawwala farashin abincin da haifar da mummunan karancin abincin a duniya.

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

Yayin da kasar Amurkar ke zargin wasu kasashe da tara hatsi, tana kuma umartar wasu kasashen da su bude ma’ajiyar abincinsu kuma su fitar da hatsin, kasar bata taba rage yawan hatsin da take amfani da su wajen samar da makamashi.

A lokaci guda kuma, tana amfanin da wannan damar wajen tsawwala farashin hatsi domin cimma wata moriya ta kashin kai. Wannan halayyar rashin kirki ne.”(Ahmad)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki
Daga Birnin Sin

Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

October 17, 2025
Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth
Daga Birnin Sin

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

October 17, 2025
Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika
Daga Birnin Sin

Sin Da Afrika Sun Yi Alkawarin Tabbatar Da Nasarar Shirin TVET Na Nahiyar Afrika

October 16, 2025
Next Post
Shugabar Sashen Lura Da Halittu Ta MDD Ta Yaba Nasarorin Da Sin Ta Samu A Fannin Kare Muhalli

Shugabar Sashen Lura Da Halittu Ta MDD Ta Yaba Nasarorin Da Sin Ta Samu A Fannin Kare Muhalli

LABARAI MASU NASABA

Mun Dakile Hari A Kano Da Ka Iya Zama Mafi Muni A Tarihin Nijeriya —Irabor

Matsalar Tsaro: Janar Irabor Ya Nemi A Sa Dokar Ta-baci A Wasu Sassan Nijeriya

October 17, 2025
Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

Tawagar Sin Ta Dindindin A Hukumar Fao Ta Fara Aiki

October 17, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Gwamnatin Kano Ta Kai Ƙarar Ganduje Da Wasu Kotu Kan Zargin Almundahanar N4.4bn

October 17, 2025
Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

Manyan Kalubalen Da Sabon Shugaban INEC Zai Fuskanta

October 17, 2025
Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

Ma’aikatar Kasuwanci Ta Kasar Sin: Sin Za Ta Kyautata Matakan Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth

October 17, 2025
A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho

Zan Tabbatar Ana Tafiyar Da Ayyuka A Tashoshin Jiragen Ruwa A Afrika Ta Yamma —Dantsoho

October 17, 2025
Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja

Dantawaye Ya Karɓi Ragamar Aiki A Matsayin Sabon Kwamishinan Ƴansandan Abuja

October 17, 2025
peter

2027: Peter Obi Ya Shiga Rudani Kan Jam’iyyar Da Zai Tsaya Takara

October 17, 2025
Ƙungiyar NNYLF Ta Gargaɗi Atiku Da Sowore Kan Cinna Wutar Rikici A Nijeriya

Ƙungiyar NNYLF Ta Gargaɗi Atiku Da Sowore Kan Cinna Wutar Rikici A Nijeriya

October 17, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilin Karyewar Farashin Kayan Abinci

October 17, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.