Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Taraba, Farfesa Joseph Albasu Kunini ya ajiye mukamin shugabancin majalisar.
Mataimakin kakakin majalisar, Alhaji Hamman Adama Abdulahi, wanda ya jagoranci zaman majalisar a safiyar Laraba, ya karanta wasikar yin murabus din Kunini mai dauke da kwanan wata 21 ga watan Disamba 2022.
- Abokan Hamayyata Ba Su Da Nagarta – Tinubu
- Yadda Zan Inganta Rayuwar Talakawan Gombe- Mailantarki Na NNPP
Ya bukaci mambobin majalisar da su zabi wani da zai maye gurbin tsohon kakakin.
Wasikar ajiye mukamin kakakin majalisar ya nuna cewa, “Bisa dalilai na kashin kaina ne na ajiye mukamin kakakin majalisar dokokin Jihar Taraba. Ina godiya ga mambobin majalisar a bisa hadin kai da goyon bayan da suka bani lokacin da nake matsayin kakakin majalisar.”
Kunini, wanda aka zaba a matsayin kakakin majalisar a ranar 2 ga watan Disamban 2019, biyo bayan ajiye aikin kakakin majalisar, Mista Abel Diah, wanda aka yi amannar ya kawo ci gaba sa majalisar.
Kazalika, Mista John Bonzana Kizito da ke wakiltar mazabar Zing, mambobin majalisar sun zabe shi a matsayin sabon kakakin da zai maye gurbin Kunini.
Da ya ke jawabi bayan rantsuwar kama aiki, Kizito ya gode wa mambobin majalisar bisa zabarsa da suka yi a matsayin wanda zai jagorancesu.
Sabon kakakin ya roki goyon baya da hadin kan mambobin majalisar domin ya samu nasarar sauke nauyin da ke kansa da kuma kai majalisar zuwa mataki na gaba.
Kizito an zabesa a matsayin dan majalisar Zing ne a 2007 kuma tun daga wannan lokacin shi yake lashe zaben daga mazabarsa hakan ya sanya shi zama dan majalisa har karo hudu.