Kakakin majalisar wakilai, Dakta Abbas Tajuddeen, ya bayyana cewa majalisa ta 10 nan ba da jimawa ba, zata waiwayi kudurin masarautun gargajiya don yin duba a kansa da kuma zartar da shi ba tare da jinkiri ba.
Tajuddeen ya bayyana haka ne lokacin da ya jagoranci shugabancin majalisar wajen wata ziyara ga sarkin Zazzau a fadarsa da ke Zariya.
- Ana Zargin Jami’in NIS Da Bindige Mai Zanga-zanga A Ogun
- Zaman Lafiya Zai Bunkasa A Kaduna -Uba Sani
Dakta Tajuddeen ya jaddada gudummuwar da masarautun gargajiya ke bayarwa wajen kawo karshen matsalolin da ke damun kasarnan, hakan kuma ya kamata a san da shi a tsarin mulkin kasa.
Abbas ya yi bayanin cewa majalisar ta 10 za ta yi tsarin yadda kowanne dan Nijeriya zai samu damar fadin albarkacin bakinsa akan abubuwan da suka shafi rayuwarsa a matsayinsa na dan kasa.
Ya nuna jin dadinsa dangane da taimakon da masarautar Zazzau ke yi da samun dama ta kasancewa dan majalisar dokoki har zuwa yanzu da ya kasance kakakin majalisa ta 10.
A yayin da ya ke jawabi, sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya nemi da a gaggauta tabbatar da kudurin domin masarautun gargajiya su samu goyon bayan kundin tsarin mulki wajen yin aikace-aikacensu a matsayinsu na shugabannin al’umma.
Sai dai Malam Ahmad Bamalli ya ba ‘yan siyasa masu rike da mukaman siyasa shawara da su guji kauracewa mazabunsu sannan kuma su hada hannu da wadanda suka fadi a zabukan da aka yi na shekarar 2023 domin samar da shirye-shirye da za su inganta rayuwar mutane a karkara.