A daidai lokacin da ake gaf da babban zaben 2023 da ya rage sauran kwanaki kalilan, akwai muhimman batutuwa da ka iya zama kalubale ga babban zaben.
A bisa wannan batun ne maka yi nazarin wasu muhimman batutuwan da suka fi zama matsala ga gudanar da zaben kai tsaye da suka kunshi karancin samun Mai, sabon tsarin sauyin kudi, matsalar tsaro da kuma dambarwar siyasa a tsakanin ‘yan takara da jam’iyyu.
Wani masani mai suna Muhammadu Ashiru ta cikin hirarsa da jaridar nan, ya shaida cewar daga cikin matsalolin da za a iya fuskanta a yayin zaben sun hada da matsalar nan ta karancin kudi a hannun jama’a da kuma babban batun nan na karancin samun Mai wanda ke matukar wahalar da jama’a a bangaren zirga-zirga da sufuri.
Ashiru wanda mai sharhi ne kan lamuran yau da gobe ya shaida cewar, “Zaben 2023 zai iya fuskantar kalubale sosai musamman ganin yadda ake fama da matsalar karancin Mai da kuma na kudi. Misali, kowa ya san hidimar zabe abu ne wanda ke janyo zirga-zirga sosai, to wannan matsalar na karancin Mai din zai iya zama kalubale ga shiga wuraren da ake son shiga walau wajen kai kayan gudanar da zaben ko kuma ga jami’an da ke sanya ido ko bada tsaro kan zabe ko kuma masu yin rakiya ga kayan zabe ko sakamakon zabe, dukkanin wadannan abubuwan da na jere ana bukatar Mai na sanyawa a motoci ko mashina wajen gudanar da su.
“Sannan, matsalar karancin kudi na iya janyo matsala, duk da tsari ne mai matukar kyau, to amma jama’a na bukatar kudade a hannunsu wajen sayen kayan bukatun rayuwa a yayin zaben ko gabani ko bayan zaben. Ta yadda karancin kudi zai shafi lamarin nan kuma, wani zai iya cewa ake taransifa a kowani lokaci wajen saye da sayarwa, to amma ya kamata kowa ya gane cewa ba komai ne za ka iya saya ka yi transfer yadda ranka yake so ba, misali achaba, sayen kayan miya, ruwa, su rage da sauran kananan abubuwan bukatuwa.
“A ma je kan transfer din, bankuna da dama suna fama da matsalar network wanda za ka iya tura kudi ma ya kashi tsawon awanni ba tare da ya shiga ba. To hakan ka iya zama matsala ga zaben da ke tafe,” ya shaida.
Ya kuma ce, akwai matsalolin tsaro a wasu yankunan da ka iya zama barazana wajen gudanar da zaben, “Ka san dai har zuwa yanzu akwai kauyuka da dama da ba za a iya gudanar da zabe a cikinsu ba sakamakon matsaloli na tsaro. Don haka akwai kalubalen da za a iya fuskanta ta bangaren tsaro.”
Bayan wannan matsalolin da ka iya bijirowa, tunin wasu ‘yan siyasa suka fara fargabar cewa ko masu rike da madafun iko za su yi amfani da karfin iko wajen abokan adawarsu domin ganin sun samu nasarar zarcewa ko kuma wadanda suke so sun yi nasara a zabukan da ke tafe.
A gefe guda ma kuma, wasu na korafin cewa jami’an tsaro ka iya taka rawa wajen mara wa jam’iyyun da ke da alaka da gwamnatin tarayya, kan haka ne gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammadu, kuma dan takarar gwamnan jihar ya bukaci jami’an tsaro da kada su yi kokarin janyo matsaloli a yayin zaben da ke tafe ta hanyar tsayawa a matsayinsu ba tare da katsalandan ba.
“Kodayake na san lokacin zabe akwai harsashen abokan adawa wadanda suke tunkaho cewa gwamnatin tarayya ta su ce za su zo su yi amfani da su, su mana barazana su zare mana idanu. Shi ya sa na musu huduba cewa kamar yadda Baba Buhari ya ce, shi na kowa ne shi kuma ba na kowa ba ne; to akwai bukatar su san cewa su huruminsu shine su tabbatar an zauna lafiya, dan sanda abokin kowa ne, ba daidai ba ne a samu wani jami’in tsaro da zai nuna bangaranci ko a kan kaina ne, a bar mu mu nema a wajen Allah a wajen al’ummar Allah mutane ba wai a je a nuna soyayya ko sun zuciya ba,” ya shaida.
Bala ya kuma nuna fargabarsa kan cewa wasu na amfani da tallafin gwamnatin tarayya wajen neman mallake zukatan masu zabe, “Shi zabe in ba ka ci ba hankalinka ba zai kwanta ba, kuma muna jin harsashen wasu ba sa kiwon ragon layya sai ranar layya suke saya. Muna jin labarin wadansu su na tanadin hatsi wanda na gwamnatin tarayya ne na tafi wanda za su zo su bayar, muna jin harsashen abubuwan da ake yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake son taimaka wa dalibai wadanda basu da aikin yi ana son a maidashi hanyar siyasa ta yadda zai kasance mutane su hau doron wannan tallafin domin mutane su zabesu, to wannan kalubale ne a garemu amma muna da hanyoyi iri-iri domin shawo kan wadannan kwanta-kwanta.”
Idan za a iya tunawa a baya-bayan nan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ce, ba za ta gudanar da zabe mai zuwa ba a rumfuna 240 ba.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu shine ya bayyana a yayin wani taro da jam’iyyun siyasa a ranar Litinin din da ta gabata a birnin Abuja, ya ce, wadannan rumfuna 240 da babu wanda ya yi rajistar kada kuri’a a cikinsu, sun warwatsu a sassan jihohin Nijeriya 28 da suka hada babban birnin tarayya, Abuja.
Shugaban na INEC ya ce, hukumar za ta fitar da cikakken jerin sunayen rumfunan zaben da lambobinsu da kuma yankunansu a matakin jihohi da kananan hukumomi.
Akwai rumfunan zabe 34 a jihar Taraba da kuma 38 a jihar Imo da babu wanda ya yi rajistar kada kuri’a a cikinsu, yayin da ake da daya zuwa 12 a sauran jihohin da sauka hada da Abuja kamar yadda INEC ta bayyana.
INEC ta ce, babu wani sabon mutun da ya yi rajistar kada kuri’a a wadannan wuraren, sannan babu wani da ya nemi a sauya masa rumfa zuwa wadannan wurare saboda dalilai na tsaro, abin da ke nufin cewa, ba za a gudanar da zabe ba a rumfunan.
A jumulce, yanzu hukumar ta INEC za ta gudanar da zaben shugaban kasa ne a ranar 25 ga wannan wata na Fabairu a rumfuna dubu 176 da 606 da ke sassan Nijeriya.
INEC, ta dauki wannan matakin ne bayan da masu kada kuri’a suka ki amincewa da su yi zabe a wurarren da mafi yawansu sababbin runfuna ne da aka kirkiro saboda matsaloli na rashin tsaro.
Rashin tsaro dai ya sanya samar da rumfunan zabe kusa da jama’a, maimakon sai sun yi doguwar tafiya. Wannan ya nuna za a samu raguwar mazabun da za a yi amfani da su a wannan zabe daga sama da runfuna zabe dubu 176 da 846 a yanzu, zuwa rumfuna dubu 176 da 606.
To sai dai fitattun ‘yan siyasu kamar Isa Tafida Mafindi na da ra’ayin cewa, babban abin bukata shi ne fitowar jama’a kuma a yi zaben cikin kwanciyar hankali. Ana fatan samun sauyi a zaben na wannan shekara a Nijeriya, musamman yadda matasa da mata da yawa suka yi rijista wadanda ke kara jajaircewa kan cewa za su tabbatar da ganin zaben nasu ya yi tasiri, abin da zai iya sauya rashin fitowa zabe daga wannan jinsi da aka dade ana gani a Nijeriyar.
Baya ga wadannan, bincikenmu ya gano mana cewa akwai yiyuwar samun matsala ta hanyar amfani da ‘yan bangar siyasa ko ‘yan daba wajen kawo cikas a yayin zabe, lura da cewa ‘yan siyasa na amfani da ‘yan barandan siyasa wajen cimma manufofinsu.
Sannan kuma a bangaren hukumar zabe, da yiyuwar a samu wasu ‘yan matsaloli na kayan na’ura ko jami’ai wadanda dukkaninsu ka iya janyo tsaiko ka kalubale ga zaben.
A wani bangare kuma, kungiyar dattawan arewa (NEF) ta nuna damuwarta kan yadda kungiyoyin masu tayar da kayar baya ke barazanar gudanar da zaben 2023 a yankin Kudu maso Gabas, inda ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tabbatar da cewa an gudanar da zabe a ko’iya a fadin kasar nan.
Don haka, kungiyar NEF ta yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya magance wannan barazana, inda ta ce shurun da shugabanni da dattawa da ‘yan siyasa daga yankin da sauran sassan Nijeriya suka yi kan barazanar da ke tattare da hatsarin babban damuwa ce ga kasar nan.
Dattawan Arewa sun ce abin ya fi tayar da hankali yadda barazanar ke biyo bayan hare-haren da ake kai wa gine-ginen gwamnati da kashe-kashe da suka hada da kashe ‘yansanda a yankin.
NEF ta yi gargadin cewa idan ba a kalubalanci abubuwan da ke faruwa ba a kan gaba, wadanda ke da hannu a cikin ayyukan rashin bin doka suna iya tsammanin za su yi nasara.
A cikin wata sanarwa da daraktan yada labaranta na kungiyar, Dakta Hakeem Baba-Ahmed ya fitar, NEF ta ce ta kasance a kan matsayinta da kuma na sauran kungiyoyin da ke kishin kasa cewa dole ne zaben 2023 ya gudana a duk fadin Nijeriya.
Ta ce duk wani yunkuri na yin katsalandan ga ‘yancin ‘yan Nijeriya wajen gudanar da zaben shugabanninsu zai zama babban cin zarafi ga diyaucin Nijeriya da kuma matakin da ya kamata a bijirewa ne.
“Yan Nijeriya na son a gudanar da sahihin zabe da kuma mika mulki cikin lumana zuwa gwamnati mai zuwa, kuma bai kamata a bar wata kungiya ta jefa al’ummar kasar cikin mawuyacin hali ta hanyar jure wa barazana ga zabe da zaman lafiya a kasar nan ba.
“Barazana ga tsarin zabe babban hadari ne ga tsarin dimokuradiyya, kuma shi ne babban ginshikin da al’umma ta dogara a kai. Idan har ta yi nasara kan wannan barazanar za ta nuna cewa an fara wasu rigingimun da kasar nan ba za ta iya farfadowa ba,” in ji ta.
Ba Mu Amince Da Gwamnatin Rigon Kwarya Ba – Afenifere
A nata bangaren kuwa, kungiyar kare muradun kabilar Yarbawa ta Afenifere ta roki Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya bijire wa duk wani yunkunrin kafa gwamnatin rikon kwarya a Nijeriya, domin kasar tana tsarin dimokuradiyya ne.
A cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Kwamared Jare Ajayi, ya fitar, kungiyar Afenifere ta ce kiran ya zama dole ne biyo bayan sanarwar da gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi, wanda wasu daga cikin fadar shugaban kasa ke yunkurin ganin shugaban ya kafa gwamnatin wucin-gadi a Nijeriya.
Kungiyar ta lura cewa wadanda ke ba da shawarar gwamnatin rikon kwarya suna yin hakan ne ta hanyar samar da yanayin da ba za a yi zabe ba.
Sai dai kuma kungiyar ta Afenifere ta ce kiran da ta yi ba ta goyi bayan gwamnan Jihar Kaduna ba ne, kawai ta bayyana muradinta ne ta bayyana.
Afenifere ta gargadin masu tunani bayar da gwamnatin rikon kwarya da su daina, saboda irin wannan tunanin babban hatsari ne ga kasar nan.