Tun bayan rantsar da Shuagaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ‘yan Nijeriya ke zakuwar ganin wadanda za su kasance shugabannin majalisar dokokin Nijeriya a karo na 10.
Ba sabon abu ba ne a Nijeriya shugaban kasa ya bayyana ‘yan takarar da yake bukata su kasance shugabanni a zauren majalisa, musamman ma a daidai lokacin da jam’iyyarsa take da gagarumin rinjaye a kujerun majalisar. Idan ba a mantaba jam’iyyar APC da Shugaban Tinubu sun nuna goyon bayansu ga wadanda suke son zama shugabannin majalisa.
- An Cafke Mai Sojan Gona A Matsayin Jami’in EFCC Da Sojoji
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Daliban Jami’ar Jos 7
A ranar Talata aka fafata zabe a zauren majalisar dokokin Nijeriya, inda aka zabi shugabani da za su ja ragamar majalisa ta 10 tare da kaddamar da ita. Bayan fafatawa dai a karshe Tsohon gwamnan Jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio ya zama sabon shugaban majalisar dattawa ta 10, yayin da Sanata Jibrin Barau dan majalisa mai wakiltar Kano ta arewa ya zama sabon mataimakain shugaban majalisar.
Akpabio ya kasance dan takarar da jam’iyyar APC ta mara wa baya. Tuni aka rantar da shi bayan ya samu kuri’u 63, yayin da abokin takararsa, Sanata Abdulaziz Yari ya samu kuri’u 46 da ‘yan majalisar suka kada.
Shin wane ne Sanata Akpabio? Tarihi ya nuna an haife shi ne a Jihar Akwa Ibom a ranar 9 ga Disamba, 1962. Ya rasa mahaifinsa tun yana karami, inda ya girma a hannun mahaifiyarsa.
Ya yi makarantar firamare ta Methodist da ke Ukana cikin karamar hukumar Essien Udim a Jihar Akwa Ibom, sannan ya yi kwalejin gwamnatin tarayya da ke garin Fatakwal na Jihar Ribas, inda ya zarce zuwa Jami’ar Kalabar ta Jihar Kuros Riba wanda a can ne ya samu digiri a fannin shari’a.
Ya yi aiki a matsayin malamin makaranta da kuma yin tarayya da wani kamfanin lauyoyi a Nijeriya. Ya kuma yi aiki da kamfanin ‘EMIS Telecoms Limited’ da wani kamfanin sadarwa a Legas. A 2002, ya kai matsayin manajan darakta na kamfanin. A baya ya taba zama akataren yada labarai na kungiyar kamfanonin sadarwa a Nijeriya (ATCOM), yayin da ya zama daraktan EMIS.
A 2002, tsohon gwamnan Jihar Akwa Ibon, Obong Bictor Attah ya nada shi a matsayin kwamishinan man Fetur da albarkatun kasa. A tsakanin 2002 zuwa 2006, ya yi aiki a matsayin kwamishina a ma’aikatu uku masu muhimmanci: Man Fetur da albarkatun kasa, kananan hukumomi da harkokin masarautu da filaye da gidaje.
A 2006, ya tsaya takarar gwamnan Jihar Akwa Ibom a zaben fid da gwani da aka fafata, inda ya doke wasu ‘yan takara 57 da suka yi takara a jam’iyyar PDP.
A yakin neman zabensa da ya yi wa taken, “Komi nufin Allah ne” ya samu goyon bayan jama’a kuma an zabe shi a matsayin gwamna a 2007. An sake zabe shi a karo na biyu a kan mulki a 2011.
A 2013 ne aka zabe shi a matsayin zababben shugaban kungiyar gwamnonin PDP. A 2015, ya tsaya takara kuma ya lashe kujerar majalisar dattawa.
- Gwagwarmayar Siyasar Akpabio
Sabon shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio, na daya daga cikin ‘yan Nijeriya masu sa’a da aka haifa, wanda ya kasance zuri’arsu sun dade a cikin harkokin mulki a kasar nan.
Akpabio ya fito ne daga gidan manyan ‘yan siyasa, kakansa, Okuku Udo Akpabio shi ne babban hakimin Warrant a lardin Ikot Ekpene a tsohuwar Nijeriya, yayin da kawunsa, Dakta Ibanga Akpabio ya taba rike mukamin ministan ilimi da harkokin cikin gida a yankin gabashin Nijeriya. Dan’uwansa, Mai shari’a Nsima Akpabio, shi ma dan majalisar dattawa ne a jamhuriyar ta biyu.
A yayin da yake takara a karkashin jam’iyyar PDP, ya samu kuri’u 422,009 daga cikin kuri’u 439,449, inda ya doke Cif Inibehe Okorie na jam’iyyar APC, wanda ya samu kuri’u 15,152 da hukumar za e mai zaman kanta ta kasa ta bayyana.
A shekarar 2015, lokacin da Akpabio ya fara rika mukami a zauren jamalisar dattawa an nada shi babban jami’i a matsayin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa.
A watan Agustan 2018, ya yi murabus a matsayin shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa bayan ya bayyana sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
- Gwagwarmayarsa Daga Majalisa Zuwa Bangaren Zartarwa
A watan Yulin 2019, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin ministan harkokin Neja Delta (NDDC), wanda aka rantsar da shi a ranar 21 ga watan Agustan 2019.
A watan Yunin 2022, burin Akpabio ya kara kaimi lokacin da ya yi murabus daga mukaminsa na ministan harkokin Neja Delta domin ya tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki, sai dai a daren ranar zaben fid da gwani na shugaban kasa ya janye wa Tinubu.
Bayan ya janye takarar kujerar shugaban kasa, Akpabio ya samu tikitin takarar sanata ne ta hanyar umarnin kotu daga mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, Mista Udom Ekpoudom mai ritaya
Bayan ya samu tikitin tsayawa takarar sanata, Akpabio ya fara fafatawa wajen neman kujerar shugabancin majalisar dattawa kuma daga karshe jam’iyyar APC ta tsayar da shi.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki zagwan kasa (EFCC) tana binciken Akpabio a kan zargin karkatar da sama da naira biliyan 100 daga Jihar Akwa Ibom a lokacin da yake gwamna tsakanin 2007 zuwa 2015 tare da jami’an diflomasiyyar Amurka da suka kira matakin cin hanci da rashawa a matsayin abin ban mamaki a lokacin mulkinsa. Ko da yake, ba a gabatar da tuhumar ba.
Wani lauya mai suna Leo Ekpenyong wanda shi ma ya tuhumi Akpabio da laifin cin hanci da rashawa, daga bisani ‘yansanda sun gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin bata masa suna.
Haka kuma a watan Afrilun 2023, Hukumar EFCC a wata wasika, ta bukaci tsohon ministan harkokin Neja Delta da ya kai kansa shalkwatarta da ke Abuja domin yi masa tambayoyi kan binciken cin hanci da rashawa da ake yi masa.
A lokacin da yake rike da mukamin ministan harkokin Neja Delta, ya yi ta ce-ce-ku-ce da ‘yan majalisar a yayin zaman kwamitin majalisar dokokin da ke gudanar da baincike a kansa.
Da aka tambayar tsohon gwamnan Akwa Ibom, ya shaida wa kwamitin cewa ‘yan majalisar dokokin kasar na da hannu wajen ba da kwangila a cikin hukumar raya Neja Delta, kuma nan take shugaban kwamitin Thomas Ereyitomi ya ce wa tsohon ministan ya yi gaggawar ajiyeye abin magana.
Nan take Akpabio ya fusata bayan taron jin ra’ayoyin jama’a, ya ci gaba da bayyana sunayen ‘yan majalisar da suka samu kwangiloli daga NDDC.
Daga bisani, Akpabio ya ki amincewa da sammacin da majalisar ta yi masa, wanda hakan ya sanya ‘yan majalisar suka yanke hukuncin cewa bai yi ladamar abin da ya aikata ba a zauren majalisar kuma yana da girman kai.
Daya daga cikin abubuwan da ke ba mutane sha’awa da Akpabio shi ne, murmushin da yake yi a ko da yaushe. Zai yi wahala ka ga Akpabio yana fushi duk abin da aka yi masa.
Hakazalika tsohon gwamnan ya shahara da iya magana, hankali da kuma nutsuwa. Kullum yana da matukar gwarin gwiwa a kan abubuwan da yake gudanarwa.
Ya auri Ekaette Akpabio, wacce ta kafa kungiyar mai zaman kanta ta ‘Family Life Enhancement Initiatibe’, da ke samar da wani dandali na mayar da hankali ga kokarin ci gaba a kan iyali a matsayin dabarun cimma burin ci gaban karni. Sun kasance suna da ‘ya’ya mata guda hudu.
A cikin jawabinsa bayan rantar da shi, Akpabio ya ce zai yi aiki da dukkan ‘yan majalisar dattawa ba tare da nuna bambanci ba. Ya yi kira da ‘yan majalisar da su ba shi goyon baya wajen ciyar dimokuradiyya gaba.
Akpabio ya bayyana kudurin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na gina tattalin arziki a matsayin abu mai kyau, inda ya kara da cewa ayyukan da ya yi a makonnin baya-bayan nan sun nuna yadda ya fahimci kalubalen da ‘yan Nijeriya ke ciki.
Akpabio ya ce majalisar dattijai ta 10 za ta samar da wasu dokoki da suka jaddada ingancin tattalin arziki tare da bayar da hadin kai ga bangaren zartarwa don aiwatar da tsarin da ake bukata.
Hakazalika, a zauren majalisar wakilai kuwa, Hon Tajudeen Abbas ya zama sabon shugaban majalisar ta 10, yayin da Benjamin Kalu dan majalisa mai wakiltar mazabar Bende daga Jihar Abiya ya zama mataimaki.
Abbas, dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Zariya da ke Jihar Kaduna ya samu kuri’u mafi rinjaye guda 353 da ‘yan majalisa suka kada a ranar Talata, inda ya samu nasarar doke Aminu Sani Jaji da Ahmed Idris Wase wanda ya samu kuri’u 3 kowannensu.
- Gwagwarmayar Sabon Shugaban Majalisar Wakilai, Hon Tajudeen Abbas
An dai haifi a Abbas ne a ranar 1 ga Oktoban 1963 a Jihar Kaduna. Ya fito ne daga Masarautar Zazzau, kuma yana da sarauta ta Iyan Zazzau.
Ya yi digirinsa na farko da na biyu a fannin gudanar da kasuwanci a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya na Jihar Kaduna a tsakanin shekarar 1988 zuwa 1993. Ya samu digirin-digirgir a fannin kula da harkokin kasuwanci a jami’ar Usman Danfodio da ke Jihar Sakwato a 2010.
A tsakanin 2001 zuwa 2005, Abbas ya yi aiki a matsayin manajan kasuwanci a kamfanin rarraba taba sigari na Nijeriya, wanda a yanzu kamfanin ya kasance na hadin gwiwa a tsakanin kasashen Ingila da Amurka.
Abbas ya tsuduma cikin harkokin siyasa gadan-gadan a shekarar 2010, inda ya tsaya takarar dan majalisar wakilai a 2011 kuma ya yi nasara.
Ya kasance dan majalisar wakilai ta takwas da ya fi kawo kuduri a zauren majalisa a tsakanin 2015 zuwa 2019, ya kawo kudurori har guda 74 daga ciki, guda 21 aka sanya wa hannu suka zama doka tsakanin 2019 zuwa 2023.
Ya yi aiki a cikin kwamitocin majalisar wakilai sama da bakwai tun a shekarar 2015 da suka hada da kasuwanci, kudi, ayyuka na musamman, tsaro, kadarorin gwamnati da kuma kwamitin tsare-tsare da bunkasa tattalin arzikin kasa.
Har zuwa lokacin da ya zama shugaban majalisar wakilai, Abbas shi ne shugaban kwamitin kula da harkokin sufuri na kasa.
Da yake gabatar da jawabinsa bayan an rantsar da shi, Abbas ya bayyana cewa karkashin shugabancinsa majalisa ta 10 za ta yi aiki tukuru fiye da majalisa ta tara.
“Za mu gudanar da aikin da ke gabanmu tare. Za mu gabatar da gyare-gyare da sabbin abubuwa don amfanin ‘yan Nijeriya.
“A cikin ‘yan makonni kadan, za mu tsara ajandar majalisar majalisar wakilai ta 10,” in ji Abbas.