Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Leeds United, Kalvin Phillips, ya kammala komawa Manchester City akan kudi Fam miliyan 45, kamar yadda kungiyar ta bayyana da safiyar yau.
Dan wasan, mai shekara 26 a duniya ya saka hannu akan yarjejeniyar shekara shida da sharadin karin shekara daya.
- Cutar Amai Da Gudawa Ta Bulla A Kano
- Ban Taba Umartar Kiristoci Su Sayi Bindiga Ba — Fasto Adeboye
Manchester City tana bukatar maye gurbin Fernandinho, wanda yabar kungiyar ya koma kasar Brazil da buga wasa wanda hakan yasa ta yanke shawarar sayan Phillips, dan kasar Ingila.
A kwanakin baya dai an danganta dan wasan da komawa Manchester United sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa Philliphs ya fi sha’awar komawa Manchester City domin yin aiki tare da kocin kungiyar, Pep Guardiola.
Dan wasan, wanda aka haifa a birnin Leeds na Ingila, shi ne na uku da kungiyar ta siya a wannan kakar bayan Erling Haaland da Julian Alvarez da zakarun na Firimiya suka dauka.