‘Yansanda sun kama shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), Joe Ajaero, a babban birnin Jihar Imo, Owerri, bayan da suka shirya gudanar da zanga-zanga.
An kama shugaban kungiyar ne dai a lokacin da yake shirin jagorantar zanga-zangar rashin amincewa da abin da suka kira da rashin mutunta ma’aikata, da gwamnatin jihar ke yi, saboda rashin biyan albashi da kudin fansho da dai sauransu.
- Dankwambo Ya Ce Daga Yanzu Gwamnatin Gombe Ta Daina Biyansa Fansho Ya Yafe
- Diphtheria: Gwamnatin Kano Ta Yi Gargadi Kan Hada Taruka
Wata majiya ta ce an kama Ajaero saboda zargin kin mutunta umarnin kotun ma’aikata, na dakatar da kungiyoyin kwadago na NLC da da TUC daga gudanar da zanga-zanga a jihar.
Sai dai a wata sanarwar da kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Okoye Henry ya fitar, ta ce ba kama Ajaero suka yi ba, sun yi hakan ne don ba shi kariya, kada wasu su cutar da shi sakamakon yadda zanga-zangar tasu ke cike da sarkakiya.
“Bayan haka kwamishinan ‘yansanda ya ba da umarnin a kai shi asibitin ‘yansanda da ke Owerri, inda za a kula da lafiyarsa sakamakon harin da aka kai masa.”
Kungiyar kwadago ta NLC a Jihar Imo, ta barranta kanta da wannan zanga-zangar da shugabancin kungiyar na kasa ya shirin gudanarwa a jihar.
Ita ma gwamnatin jihar Imo ta ce babu hannunta game da kama Ajaero da aka yi, inda kwamishinan yada labarai na jihar, Declan Emelumba, ya ce yanyi mamakin abinnda ya kai shi jihar don gudanar da zanga-zangar da ta sabanwa umarnin kotu.