Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, Ya bayyana ra’ayin sa kan wanda yake so ya gaji Shugaba Buhari, inda ya furta cewa ya kamata Jam’iyyar su APC ta cika Alkawarin ba wa yankin kudancin Nijeriya mulki a kakar zaben shekarar 2023.
Sanata Gaya ya bayyana hakan ne a wata Hira da yayi da Kamfanin yada labarai na BBC.
Tun a farko, Rahotanni sun nuna cewa, anji rade-raden rashin jituwa a tsakanin Gwamnoni APC gabanin Zaben fidda gwani na dan takarar Shugaban Kasa, biyo bayan ganawar da Shugaba Buhari yayi da gwamnoni kan neman su da su mara wa Wanda Shugaban yake so ya gaje shi.
Sai dai rahotanni sun ce wadannan kalamai ba su yi wa wasu gwamnonin dadi ba.
Sanata Gaya ya ce: “Ita siyasa, ko ma duk rayuwar duniya, alkawari ce. Idan ka yi wa dan Adam alkawari, to ka cika alkawarin da ka yi da shi. An yi alkawari da kudu cewa su amince Buhari ya yi mulkin shekara takwas, ya kamata kuma a mika musu, domin su ma su yi shekara takwas.”