Kamfanin hakar ma’adinai, Prateek Suri’s, ta sanar da shirinta na rungumar fasaha domin tabbatar da inganta ayyukan da suka shafi hakar ma’adinai.
A wata sanarwa da kamfanin ta fitar a Afrika, na cewa, ba kawai zallar hakowar ba, akwai bukatar zurfafa tunani da yin amfani da fasaha wajen kyautata hakowar da kuma daurewarsa.
- Kakakin Majalisa Ga Tinubu: Ka Dauki Kwararan Matakai Kan Karuwar Matsalolin Tsaro
- Bikin Al’adun Gargajiya Na Rigata Karo na 3 Zai Gudana A 8 Ga Fabrairu A Yauri
Sanarwar na cewa, “Tare da alkawarin yin amfani da na’urorin zamani da fasahohi, Suri’s ya dukufa wajen sauya yanayin hakar ma’adinai daga matakin da aka saba zuwa na zamani.”
Kamfanin ta kara da cewa nahiyar Afrika na da albarkatu da dama kama daga karafa, madinai da kuma albarkatun makamashi, tare da karawa da cewa, duk da wadannan tagomashin, sha’anin hakar ma’adinai na fuskantar tulin matsaloli, ciki har da amfani da wuraren da aka daina yayinsu, tsarika masu rikitarwa, da farashi marasa tabbas.
Sanarwar na karawa da cewa, “Kamfanin Prateek Suri ya fahimci wadannan matsalolin a matsayin damarmakin da za a bi wajen bullo da dabarbatun da za a yi amfani da su wajen cigaba a nan gaba da kuma kyautata harkokin hakar ma’adinai a nahiyar Afrika. Nijeriya da ke da albarkatun kasa sosai ta zama babban wurin da kamfanin Prateek ya sanya tunaninsa da burinsa a kai.”
Kamfanin ya ce, bisa halin da ake ciki, tabbas amfani da fasaha zai taimaka matuka gaya wajen kyautata harkokin ma’adinai da kuma rage shiga cikin hatsari da masu hakar ma’adinai ke yi.