A ranar Litinin kamfanin Air Peace ya sanar da dakatar da ayyukansa na Dubai saboda ‘Yan Nijeriya sun gaza samun biza zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
A cikin wata sanarwar manema labarai da hukumar Air Peace ta fitar, kamfanin ya ce za a dakatar da ayyukansa daga ranar Talata 22 ga watan Nuwamba, 2022.
- An Jinjinawa Matakan Sin Na Shawo Kan Kalubalen Sauyin Yanayi
- Zulum Ya Raba Abinci Da Atamfa Na Miliyan 255 Ga Talakawa 70,000
Sanarwar ta ce, “Muna sanar da jama’a, musamman fasinjojinmu na Dubai, cewa daga ranar Talata 22 ga watan Nuwamba, 2022, za mu dakatar da ayyukanmu na Dubai har sai an sanar da mu.
“Hakan ya faru ne sakamakon rashin bayar da biza ga matafiya ‘yan Nijeriya da gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ke ci gaba da yi da kuma matsalolin da suka biyo baya.
“Za mu ba da ƙarin bayani yayin da lamarin ke ci gaba. Fasinjoji waɗanda wannan lamarin ya shafa za su iya tuntubarmu ta [email protected]
LEADERSHIP ta rawaito cewa, a watan Oktoba, 2022, Hadaddiyar Daular Larabawa ta bayar da sanarwa ga abokan huldar kasuwancinta a Nijeriya, ciki har da wakilan tafiye-tafiye kan hana ‘yan Nijeriya biza.