Kamfanin sumunti na BUA, ya tallafawa asibitoci 15 da magunguna da kayan asibiti tare da bayar da sumunti ga garuruwa 68 da kayan karatu ga makarantu da kayan makaranta ga dalibai a Sakkwato.
Daraktan Gudanarwa na BUA, Alhaji Yusuf Binji wanda mataimakin darakta kuma shugaban sashen mulki da hulda da jama’a, Sada Sulaiman ya wakilta ne ya hannun ta tallafin ga al’ummar da suka amfana a Karamar Hukumar Wamakko. Ya ce jimilar adadin kudin kayan sun kama naira miliyan 115.
- Fintiri Ya Sanya Dokar Hana fita Awa 24 A Adamawa
- Sanata Lamido Ya Ba Da Tallafin Naira Miliyan 40 Ga Daliban Jihar Sokoto
Ya bayyana cewar kayan na asibiti za su baiwa al’umma damar amfana da su a cikin sauki a ciibiyoyin kiyon lafiya a matakin farko ba tare da biyan kudi ba. Asibitocin da suka samu tallafin sune; Kalambaina, Sabon Garin Alu, Bakin- Kusu, Farfaru, Arkila, Gumbi, Faderal Low Cost, Mobile Police, Beni, Asare, Kauran Mallam Buba, Wamakko, Wajeke, Gidan Boka da Sabon Gidan Belu.
A cewarsa kamfanin ya bayar da kayan ne a bisa ga marawa kokarin gwamnati baya a fannonin kiyon lafiya, ilimi da ci-gaban al’umma.
Ya ce kungiyoyin ci-gaban al’umma 68 ne suka samu gudunmuwar buhunan sumunti domin gudanar da ayyukan gyaran masallatai, makabartu, magudanan ruwa da sauraren muhimman wuraren da al’umma ke bukatar gyarawa.
Ya ce kamfanin ya kuma bayar da tallafin karatu ga dalibai 158 ‘yan asalin Jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara, haka ma kimanin yara ‘yan makarantar furamare 1, 004 ne suka samu kayan makaranta biyu kowanne.