Reshen kamfanin sadarwa na Huawei na kasar Sin dake Habasha, ya shirya bikin baje ayyukan yi zagaye na biyu a Bahir Dar, babban birnin yankin Amhara na kasar, domin hada daliban da suka kammala karatun jami’a da bangaren fasahar sadarwa na kasar.
Bikin na gabatar da ayyuka ya gudana ne daga ranar 24 ga watan Augusta zuwa 25, da zummar lalubo masu basira a kasar. Kamfanin Huawei ya shirya bikin ne da hadin gwiwar jami’ar Bahir Dar da sauran abokan hulda, domin tallata ayyukan yi ga daliban da suka kammala jami’a.
Sanarwar da kamfanin ya fitar jiya, ta ce bikin ya ja hankalin wadanda suka kammala karatu daga jami’o’in Bahir Dar da Gondar da Enjibara da Debark, inda aka karbi takardun neman aiki sama da 800 daga mahalarta.
A cewar sanarwar, za a zabi wadanda suka fi dacewa daga takardun da suka mika, kuma za a ba su damar aiki a kamfanin. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp