A jiya ne, kamfanin fasahar sadarwa na kasar Sin wato Huawei, ya kaddamar da wata sabuwar fasahar intanet mai suna Wi-Fi 7 ga kasuwannin gabashin Afirka, a wani mataki na kawo sauyi ga hanyoyin sadarwar intanet.
Babban jami’in fasahar kamfanin mai kula da yankin kudancin Afirka Matamela Mashau, ya shaidawa manema labarai a Nairobi, babban birnin kasar Kenya cewa, sabuwar fasahar, ta samo asali ne sakamakon bukatar masu amfani da fasahar na saurin saukarwa da loda bayanai da kuma bukatar hada na’urori da dama zuwa ga Intanet din.
Mashau ya bayana cewa, fasahar Wi-Fi 7 ta ninka adadin na’urorin da za su iya aiki yadda ya kamata, tare da intanet mai saurin gaske, da kuma tabbatar da cewa, a gida ko kuma a ofis na iya daukar har zuwa na’urorin talabijin na zamani 120, da kwamfutoci da wayoyi a kowane lokaci.
Ya bayyana cewa, fasahar ta Wi-Fi 7 wani sabon tsari ne na masu amfani da hanyar sadarwa wanda ke kawo wa kasuwa, tsarin intanet mafi sauri da gudun da ya kai 500Mps ga kowace na’ura da kuma saurin da ya kai Gigabits 30 a cikin dakika 1.
Kaddamar da wannan shirin na zuwa ne, a daidai gabar da gwamnatin Kenya ke ci gaba da kokarin zurfafa amfani da intanet, ta hanyar kafa cibiyoyin fasaha a fadin kasar.(Ibrahim)