Nijeriya ta rabauta da samun jarin dalar Amurka miliyan 600, don samar da kayayyakin aiki a tashar jiragen ruwa daga kam-fanin jigilar kayayyaki na Kasar Denmark A.P. Moller- MAERSKb, kamar yadda fadar shugaban kasa ta fitar da sanar-war.
Har ila yau, an samu wannan nasara ta shirin zuba jarin ne a wata ganawa da aka yi tsakanin Shugaba Kasa Bola Ahmed Tinubu da Shugaban kamfanin na Moller-Maersk, Robert Maersk Uggla; a yayin gudanar da taron tattalin arziki na duni-ya da aka yi a kasar Saudiyya.
- NPA Ta Kashe Fiye Da Dala Miliyan 200 Wajen Yashe Tashoshi Jiragen Ruwa A Legas
- Majalisar Kasa Ta Bayyana Dalilan Watsi Da Zarge-zargen Badakalar Naira Biliyan 178 A Kan Shugaban NPA
“Mun aminta da Nijeriya, za kuma mu zuba jari na akalla dala miliyan 600; a kan kayayyakin da ake da su, sannan kuma za mu sanya tashoshin jiragen ruwa su kasance masu dauka tare da jigilar manyan jiragen ruwa”, a cewar Uggla yayin gudanar da taron.
Kamar yadda aka sani ne, Nijeriya ta sha alwashin bunkasa tare da gyara tashoshin jiragen ruwanta, ciki kuwa har da ta birnin Legas, wato babban birnin kasuwancin kasar; domin sake rage cunkoson da ke kawo matsaloli daban-daban ga harkokin kasuwanci a fadin jihar.
Haka zalika, shi ma Shugaba Tinubu; ya bayyana gwamnatinsa; a matsayin wadda za ta tallafa tare da inganta wadannan tashoshin jiragen ruwan, domin bunkasa harkokin kasuwanci kasar da kuma kokarin rage matsalar cin hanci da rashawa tare kuma da inganta ayyuka tashoshin yadda ya kamata.