Kamfanin gine-gine na kasar Sin (CCECC) ya kaddamar da fara aiki a hukumance na wani muhimmin titin da aka tsara don inganta hanyoyin shiga yankunan karkara da aka yi biris da su a babban birnin tarayyar Nijeriya.
Aikin titin mai tsawon kilomita 7 a kauyen Tungar Madaki da wasu kauyuka da ke makwabtaka da juna a babban birnin tarayyar Nijeriya Abuja, ya kunshi duk wasu sassa na ayyukan gina titi, kamar yadda Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja ya bayyana a wajen bikin kaddamar da fara aikin a ranar Litinin.
Wike ya kara da cewa, aikin titin “yana da matukar muhimmanci” kuma “ya yi daidai da ajandar sabunta kyakkyawan fata” da ke cikin shirin gwamnatin Nijeriya na samar da ababen more rayuwa, kana ya yi nuni da aniyarsu ta shigar da kauyukan da aka shamakance a baya cikin ainihin tsarin raya babban birnin kasar.
A cewar Wike, ana sa ran kamfanin CCECC zai kammala aikin gabanin kaddamar da fara amfani da titin nan da watan Yunin shekarar 2026. Tsarin aikin ya kunshi komai da komai, ba kawai shimfida titin ba har ma da gada mai ginshikai guda hudu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp