Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL) ya yi wa dukkan manyan ma’aikatansa da ya rage musu kasa da watanni 15 barin aiki ritayar dole.
A Wata sanarwa dauke da sa hannun shugabannin kamfanin mai kwanan wata 18 ga Satumba, 2023 kuma aka wallafa a shafin sada zumunta na X (Twitter) da sanyin safiyar Talata, ta bayyana cewa, ritayar ta fara aiki ne nan ta ke daga ranar Talata 19 ga Satumba, 2023.
Ta kara da cewa, yanke wannan hukunci ya zama wajibi domin habbaka tsare-tsare da za su kai ga cimma nasarar da kamfanin na NNPCL ke bukata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp