Wannan hadin guiwa ne tsakanin Hukumar OSP da Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur ta Nijeriya, wannan wani yunkuri ne na inganta hanyoyin samar da tsaftataccen makamashin dafa abinci da samar da ayyukan yi a Nijeriya, musamman a Jihar Edo.
Shirin zai bunkasa yadda za’a wayar da kan al’umma da kuma horar da su a cikin gidajensu da kuma nuna musu wasu dabaru da hanyoyi da ake bi wajen inganta dahuwar abinci da ma wanda ake amfani da su a cikin gida.
- Minista Ya Nemi ‘Yan Kasuwa Su Zuba Jari Don Habaka Kasuwancin Iskar Gas Na CNG
- Jihar Bauchi Ta Lashe Lambar Yabon Kwazo A Bangaren Mai Da Iskar Gas
Shirin na OSP din ya yi daidai da shirin da Nijeriya ke da shi na samar da LPG domin ragewa yan kasa hanyoyin rage kashe kudaden da suke wajen samun makamashin da za su yi amfani da shi.
Wannan zai taimaka wajen rage yanayin dumamar yanayi da kuma samar da tsaftataccen muhalli.
Yin amfani da makamashi irin su gawayi da itace da kuma kananzir na haifar da illa mai yawa a cikin muhalli, wannan ne yasa kasar Saudiya da Nijeriya ke son kawar da irin wannan illar da wadannan makamashin suka kawo wa da tabbatar da an yi amfani da irin su LPG.
Shigar da Nijeriya cikin wannan shirin yana nuna kyakkawar manufofin dorewa da gudummawa da kasar ke bayarwa a duniya don magance ƙalubalen da suka shafi amfani da makamashi mai cutarwa.