Kamfanin PowerChina, mallakin gwamnatin kasar Sin, ya samar da gudummawar sama da na’urorin samar da wutar lantarki mai aiki da hasken rana guda 500 ga kauyen Lauteye na karamar hukumar Bunkure a jihar Kano dake yankin arewacin Najeriya.
Babban wakilin kamfanin ChinaPower a Najeriya Tian Yuan, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, manufar tallafin ita ce, aiwatar da shirin nan mai suna “kamfanoni 100 a kauyuka dubu 1” wanda kungiyar hadin gwiwar ’yan kasuwar kasar Sin a Afirka ta kirkiro don raya zamantakewar al’umma.
Shi ma shugaban karamar hukumar Bunkure AbdulRauf Umar Gadabu, ya shaidawa Xinhua cewa, gidaje da dama a yankin ba su da hasken wutar lantarki, don haka wadannan na’urori da kamfanin kasar Sin ya samar, za su taimaka wajen inganta tsaro da ma jin dadin al’umma, da ci gaban yara, domin a cewarsa, yaran za su rika amfani da hasken lantarkin da dare wajen fadada harkokinsu na ilimi.
Ana fatan taimakon kamfanin na kasar Sin, zai kawo karshen dogon tarihi na dogaro da wutar gawayi ko fitilu na kalanzir da mazauna kauyen ke amfani da su, don samun haske da dare.
Daga yanzu sama da iyalai 300 a kauyen, za su samu hasken lantarki mai tsafta da dorewa kuma kyauta da dare. (Ibrahim)