Kamfanin Simintin Dangote ya ƙaddamar da wani shirin tallafa wa manoma a jihar Benue, da nufin goyon bayan gwamnatin tarayya wajen samar da isasshen abinci a ƙasa. Shirin, wanda aka fara a ƙaramar hukumar Gboko, ya mayar da hankali ne kan ƙarfafawa manoma 50 domin su riƙa noma amfanin gona don riba kuma da amfani na gida a matakin kasuwanci.
Babban Manajan hulɗar da jama’a na kamfanin, Johnson Kor, ya bayyana shirin a matsayin babban abin tarihi da kuma sabuwar hanya ta kawo ci gaba da haɗin gwuiwa tsakanin kamfanin da al’ummomin da ke kewaye da masana’antar Simintin Dangote a Gboko. Ya ce an zaɓi manoman ne daga yankunan da ke cikin yarjejeniyar ci gaban al’umma (CDA), wanda aka rattaba hannu a kai a watan Disamban 2024.
- Matatar Dangote Za Ta Fara Dakon Man Fetur Da Dizal Kyauta A Fadin Nijeriya
- Matatar Dangote Zata Fara Rarraba Man Fetur Da Dizal A Nijeriya
Shirin zai haɗa da bayar da kayan aikin gona kamar taki, da magungunan kashe kwari, da injinan feshi da iri daban-daban. Daraktan masana’antar, Munusamy Murugan, wanda Engr Soom Kiishi ya wakilta, ya bayyana cewa wannan ne farkon tsarin tallafin, kuma ana shirin yin hakan a duk shekara, duk da cewa nau’in shirin zai iya bambanta bisa buƙatar al’ummomin da abin ya shafa.
Bayan haka, kamfanin ya bayyana cewa wasu shirye-shiryen ci gaban matasa za su biyo baya, ciki har da horo a fannin walda da haɗa na’urorin hasken rana. Haka kuma, tsarin tallafin karatu na kamfanin ya ƙunshi ɗalibai daga fannoni daban-daban a jami’o’i da kwalejoji.
A jawabin godiya, wani mutumin yankin, Kwaghgba Isaac, ya yaba da shirin, yana mai cewa hakan zai ƙara ƙarfafa noman abinci da rage yunwa a ƙasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp