Kamfanin Simiti na Dangote ta hanyar wajen da ake sarrafa masa Simitin da ke a Obajana da ke a jihar Kogi, ya kaddamar da shirye-shiryen, tallafawa masara karfi, ciki har da marayu da ke a yankin
Ya gudanar da haka ne, a shirinsa na mako na wannan shekarar tallafawa.
- An Yanke Wa Mai Haƙar Ma’adanai Hukuncin Shekara 1 Saboda Satar Waya
- ‘Yan Bindiga Ba Su Karɓe Sansanin Horo Da Ke Neja Ba – Hedikwatar Tsaro
Babban jami’i a sashen inganta rayuwar alumma a kamfanin Simitin na Dangote Eseosa Ighile, ya bayyana haka a cikin sanarwar da ya fitar.
Eseosa ya ce, kamfanin ya wannan aikin na jin kai ne, bisa maufar inganta rayuwar alummar yankin.
Duk a cikin bikin na makon, tawagar Zakarun ta Obajana, sun ziyarci ma’aiktar kula da walwalar da jin dadin marayu da ke Lokoja, babban birnin jihar, inda suka raba masu wasu kayan bukata na yau da kullum da kuma abinci kyauta.
Kazalika, sun kuma shafe lokuta tare da marayun, inda suka shakata da su, tare da yin wasa da su.
Babban jami’i ya sanar da cewa, shirin bai wai zai karfafa huddar zumunci a tsakanin kamfanin Simintin na Dangote da kuma marayn da ke zaune a gidan marayun, har da kuma kara daukaka hazakar ma’aiktan kamfanin, wajen kara janyo alumar yankin a jiki.
Makuntan gidan marayun sun nuna jin dadinsu a kan tallafin kayan.
Shi ma a na sa jawabin Darakatar da ke sa ido a wajen da ake sarrafa masa Simitin Azad Nawabuddin, ya sanar da cewa, taron na makon na da matukar mahimmanci.
Nawabuddin ya sanar da cewa, taron na 2024, an tsara za a gudanar da ayyuka da dama, na jin kan jama’a.
Kazalika, ya bayyana cewa, kamfanin zai kuma yi amfani da damar taron na mako, wajen fadakarwa da kuma ilimantarda alummar yankin, dangane da kalubalen dumamar yanayi da sauran abubuwan da suka shafi lafiyar ‘yan Adam.