Kamfanin Dandalin Twitter ya maye gurbin tambarin tsuntsu da tambarin X a matsayin wani bangare na sake fasalin dandalin.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, mamallakin shafin Twitter Elon Musk a baya, ya bayyana shirin sake fasalin dandalin tare da kawar da tambarin dandalin.
A cikin wani rahoto da ya fitar a ranar Lahadi, Elon Musk ya ce, “Yanzu X.com ya maye gurbin twitter.com”. “Tambarin X zai maye gurbin tsuntsu”
Musk ya kuma bayyana cewa, an kawata sabon tambarin X a hedkwatar Twitter da ke San Francisco, California ta kasar Amurka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp