Rahotanni daga Najeriya na cewa, kamfanin kera motocin bas-bas na kasar Sin mai suna Yutong, ya kaddamar da motocin bas na farko da za su rika jigilar jama’a a Legas, cibiyar tattalin arzikin Najeriya jiya Talata, a gabar da kasar ke shirin canjawa sannu a hankali, daga motocin da ke amfani da injina zuwa motoci masu amfani da wutar lantarki mai dorewa (EV).
Wannan aikin hadin gwiwa ne tsakanin kamfanin Oando Clean Energy Limited, dake hulda da kamfanin Yutong a Najeriya, da hukumar sufuri ta birnin Legas don fara yin gwaji da motocin Yutong guda biyu masu amfani da wutar lantarki a kan hanyar da motocin bas-bas ke bi a birnin Legas.
A cewar gwamnan jihar Legas Babajide Sanwoolu, tsarin zirga-zirgar jama’a a kasar yana da burin taka rawar gani, wajen rage hayakin Carbon. Ya ce sabbin motocin bas din masu amfani da wutar lantarki, za su rage hayakin Carbon da kuma kara ingancin harkokin sufuri. (Ibrahim)