An fuskanci fadi-tashi a fannin tattalin arziki a shekarar 2023, masana na da ra’ayin cewa, in har ana son a sake yi wa tattalin arzikin Nijeriya alkibla dole a sake fasalin tafiyar da tattalin arzikin kasar ta hanyar karfafa masana’antunmu a kuma rage dogaro ga kayayyakin da ake sarrafawa a kasashen waje wannan ne zai bunkasa tare da daukaka darajar Naira a kasuewannin duniya.
Masanann sun yi hasashen kamfanonin da za su tabuka abin arziki a cikin wannan shekarar ta 2024, kamfanonin sun kuma hada da.
Matatar Mai Ta Dangote
All’ummar Nijeraiya sun yi murnar da fara aikin matatar man Daangote a da aka kashe fiye da Dala biliyan 19 wajen kafawa, wannan kuma a bayyane yake ganin irin halin matsin da aka shiga sakamakon cire tallafin mai da gwamnantin Bola Tinubu ta yi.
Kwanaki ne kamfanin ya bayyana cewa, ya karbi danyen mai sampurin Agbami ta hannun kamfanonin MT ALMI wanda hakan ya taimaka musu gama shirye-shiryen fara aikin gwaji. Ana sa ran matatar man za ta tace gangan mai 650,000 wanda hakan zai rage dogaro da Nijeriya take yi da tataccen mai daga kasashen waje, fara aikin matatar mai na Dangote zai samar da ayyukan yi ga dimbin matasanmu zai kuma bayar da gaggaurumar gudummawa ga tattalin arzikin Nijeriya.
Kamfanin Siminti Na BUA
Kamfanin siminti na BUA zai fara sarrafa siminti tan miliyan 6 kari akan abin da yake sarrafawa a baya, tabbas wannan zai samar da gaggarumin canji ga tattalin arzkin kasa a shekarar 2024, musamman ganin hakan na nufin karin ma’aikata da kuma karin kudin shiga ga kamfanin.
Shugaban kamfani siminti na BUA, Abdul Samad Rabiu, ya ce wannan karin da kamfanin ya yi zai taimaka wajen samar da isassshen siminti a Nijeriya dama sassan nahiyar Afirka.
May & Baker
Wannan kamfanin hada magungunan ya yi alkawarin kaddamar da sabbin kayayyaki har guda 7 a wannan sabuwar shekarar ta 2024.
Tabbas kamfanin ‘May & Baker Nigeria’ na daya daga cikin kamfanonin da za su tabuka abin arziki a shekarar 2024 musamman ganin akwia gibi mai girma da za su cika bayan ficewar kamfanin hada magunguna na GSK a shekarar 2023.
Bayani ya nuna yadda fasahin magunguna suka yi tashin gwauron zabi bayan ficewar kamfanin GSK abin kuma da zai dora nauyin a kan kamfanin na May & Baker.
Seplat ANOH Gas
Ana sa ran wannan kamfanin zai rage yadda Nijeriya ke barnatar da iskar gas ya kuma taimaka wajen samar da issashen iskar gas a kasuwannin Nijeriya.
Kamfanin gas na ANOH hadaka ce tsakanin ta da kamfanin mai na NNPCL sun kuma samar da karkkarfar kamfanin da zai yi gogayya wajen cin kasuwar samar da iskar gas a fadin tarayyar Nijeriya.
Matatun Mai Na Fatakwal, Warri da Kaduna
A nasa ran matatun mai 4 da ke Nijeriya su fara aiki a cikin shekarar 2024, a halin yanzu matatar mai na Fatakwal ya fara aiki a watan Janairu.
Tun a shekarar 2022 aka shirya matatar mai na Fatakwal zai fara aiki amma saboda rashin kammala yi wa matatar garambawul lamarin ya kai zuwa yanzu.
Idan matatun man suka fara aiki yadda ya kamata, Nijeriya na fatan kawo karshen shigo da tataccen man fetur da dangoginsu daga kasashen waje, wanda haka zai karfafa tare da bunkasa tattalihn arzikin kasa
Kamfanin Mai Na A A Rano
Kamfanion mai na AA Rano ya yi fice a harkar samar da man fetur da dangoginsu. Shugaban Kamfanin, Alhaji Awwalu Rano haifaffen Jihar Kano ya kafa kamfanin ne a shekarar 1996 ya kuma zama cikakken kamfani a shekarar 2002. Kamfanin na da fiye da manyan motocin dakon fetur 600 yana kuma da gidajen mai fiye 115 a fadin kasar nan.
Haka kuma kamfanin ya shiga harkar zirga-zirgar jiragen sama in da a halin yanzu suke zirga-zirga a tsakanin garuruwan Abuja, Kano, Legas, Sokoto, Maiduguri, Kaduna, Yola da Asaba.