Kakakin kwamitin kara azama kan cinikin kasa da kasa na kasar Sin Feng Yaoxiang ya bayyana a gun taron manema labaru da kwamitin ya gudanar a jiya cewa, Sin ta gabatar da jerin manufofin tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin kasar, wadanda suka taimaka wajen kara yin imani ga kasuwar kasar, da kyautata yanayin cinikayya, kuma kamfanoni masu jarin waje suna kara nuna gamsuwa ga manufofin.
A yayin taron manema labarun, an gabatar da rahoton binciken yanayin cinikayyar kamfanoni masu jarin waje a kasar Sin a rubu’i na biyu na shekarar 2022, inda aka shaida cewa, kamfanoni masu jerin waje, sun nuna kyakkyawar fata ga bunkasuwar kasar Sin da kasuwar kasar, da kuma nuna gamsuwa ga yanayin cinikayya a Sin da kuma manufofin raya tattalin arzikin Sin.
Kusan kashi 90 cikin kashi dari na kamfanoni masu jarin waje, sun nuna gamsuwa ga manufofin samun wurin yin kasuwanci, da biyan haraji, da samun iznin shiga kasuwa, da manufofin kudi da rage haraji, da taimakawa kamfanonin wajen tinkarar yanayi mai sarkakiya yayin da ake yaki da cutar COVID-19, da kuma saukin aiwatar da manyan ayyuka masu amfani da jarin waje a kasar Sin. (Zainab)