Ganin yadda take kara aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje ta fannin hada-hadar kudi a zahirance, kasar Sin tana fadada bude kofarta ga kasashen ketare a fannin hada-hadar kudi yadda ya kamata, kana ana gaggauta kafa wani tsarin kudi dake bude wa juna kofa, wanda ba taimakawa kamfanonin kasar Sin fita waje kawai yake yi ba, har ma yana taimakawa sosai ga shigowa da kyakkyawan jarin waje a kasar ta Sin, da zummar shiga cikin ayyukan raya kasuwar hada-hadar kudi ta kasar, da more damammakin ci gaba tare.
Kididdiga ta nuna cewa, zuwa karshen watan Yunin shekarar da muke ciki, bankunan jarin waje sun kafa cibiyoyinsu guda 41, da rassansu 116 gami da ofisoshin wakilcinsu guda 127 a duk fadin kasar Sin, kana kuma jimillar kadarorin da suke da su a kasar Sin ta kai kudin kasar Yuan tiriliyan 3.87. Kaza lika, kamfanonin inshora na kasashen waje sun kafa cibiyoyin inshorarsu guda 67 a kasar Sin, kuma jimillar kadarorin da suke da su a kasar ta kai Yuan tiriliyan 2.67. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp