Kungiyar kamfanonin hada magunguna ta nemi tallafin naira biliyan 600 daga gwanmnatin tarayya don karfafa kananan kamfanonin hada magunguna a fadin tarayyar Nijeriya.
A ranar Litinin kungiyar ta yi wannann kiran a taron karrama minitan lafiya Farfesa Muhammad Fate da aka yi a Abuja.
- Abuja Na Fuskantar Baranazar Tsaro -Majalisar Dattawa
- Kotu Ta Umarci Gwamnatin Tarayya Ta Kayyade Farashin Kayayyaki Cikin Kwanaki 7
Kungiyar ta bayyan cewa, in kudaden sun samu zai tamaka wajen bunkasa harkokin kananan kamfanoni masu hada magunguna da kuma bangaren masu bincike a cibiyoyin bincike a fadin kasar nan.
A jawabinsa yayin taron, shugaban kungiyar, Dr. Okey Akpa, ya fito da mastalolin da suke kawo cikas ga bunkasar kamfanonin hada magunguna a Nijeriya.
Ya ce, kudaden za su karfafa kamfanonin hada magunguna hakan kuma zai rage tsadar magunguna tare wadata magunguna na kasuwanninmu ta yadda al’umma za su samu magunguna a cikin sauki da kuma a wadace.
Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya ta daiuki matakan kawo karshen matsalolin da kamfanonin hada magunguna ke fuskanta da kuma karancin magunguna da tsadarsu da ake fuskanta.
Akpa ya kuma ce, cikin matsalolin da ake fuskanta sun hada da yadda aka kayyade musu yawan kudaden waje da za su iya samu daga babban banki (CBN) da kuma bukatar a yi wa tsarin sayen kayayyaki daga kasashen waje kwaskwarima don masu hada magunguna su samu saukin zirga-zirgar wajen shigo da kayan aiki da kuma bukatar a rage musu wasu harajin da aka kakaba musu a matakin gwamnatin tarayya da na jihohi.
A shekaarr 2023, kamfain hada magunguna na kasar Birtaniya, GladoSmithKline, ya sanar da ficewarsa daga kasar nan bayan shekasra 51 yana harkokinsa, wasu kamfanonin ma sun bayyana aniyarsa na fita daga kasar saboda mastalar matsin tattaliin arziki da Nijeriya ke fuskanta.
A kan haka, Akpa ya nemi a dukkan masu ruwa da tsaki su hada kai don samar da mafita daga wannan mastalar don a ceto al’umma daga wahalhalun da suke fuskanta a bangaren magunguna.