An bude cibiyar kirkire-kirkire da ilimin zirga-zirgar jiragen ruwa ta farko, karkashin jagorancin kamfanonin kasar Sin, jiya Alhamis a birnin Djibouti City na kasar Djibouti.
Taken cibiyar shi ne, kirkire-kirkire na zamani da cinikayya ta intanet tsakanin kasa da kasa.
Kusan mutane 30 daga kasashen Djibouti da Habasha da Kenya da Uganda ne aka zaba domin su karbi horon na kwanaki 8. Kuma yayin horon, matasan za su koyi darussan tafiyar da harkokin kamfani, kana za a gabatar da lokaci da tarukan karawa juna sani daga masanan Sin da Afrika tare da ziyartar tashar jiragen ruwa ta Doraleh da yankin cikin cikin ’yanci na kasa da kasa na Djibouti da kamfanonin kasar Sin suka gina.
Cibiyar da aka kafa ba don riba ba, na da nufin inganta bunkasa kwarewar matasa da dabarun shugabanci da ilimin sana’o’i tsakanin matasan Djiboutu da na gabashin Afrika.
Haka kuma za ta bayar da gudunmawa ga burin da Djibouti ke son cimmawa zuwa 2035, domin bunkasa kirkire kirkire a bangarori masu zaman kansu da dogaro da kai.
Cibiyar wadda ’yan kasuwar kasar Sin suka samar da kudin kafa ta yayin da kungiyar ’yan kasuwar Sin dake Djibouti ke tafiyar da ita, za ta zama dandalin samar da hidimomi kamar na horo da bayar da shawarwari da hada ’yan kasuwa. (Mai Fassarawa: Fa’iza Mustapha)