“Masu sayayya na kasar Sin na son sabbin abubuwa da sauyi, kuma muna bukatar masu ci gaba habaka harkokinsu a nan.” Mataimakin shugaban kamfanin Unilever Zeng Xiwen ne ya bayyana haka, yayin baje kolin cinikayya da zuba jari karo na 25 da aka kammala a baya bayan nan. Shugabannin kamfanonin kasa da kasa da dama ne suka halarci taron tare da bayyana kudurinsu na daukar manufofi masu dogon zango a kasar Sin, inda suka yi amana cewa, wajibi ne su ma harkokin kasuwanci da suka tsaya da kafafunsu, su ci gaba da kirkiro sabbin abubuwa domin tafiya tare da ci gaba mai inganci na kasar Sin.
Karin damarmaki na kara bullowa ga kamfanoni kasashen waje a kasar Sin. Yanzu haka ana gudanar da baje kolin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na 2025 a birnin Beijing, kuma a watan Nuwamba, za a gudanar da baje kolin kayayyakin kasa da kasa da ake shigo da su kasar Sin karo na 8 a birnin Shanghai. Kamar yadda wakilan kamfanonin kasa da kasa suka bayyana, kasuwar kasar Sin ta zama wata cibiyar samun kuzari da karfi ga kamfanonin kasashen waje. Kuma sai sun samu karfi da damar takara a kasar Sin, kafin su kara samun nasarar shiga kasuwar duniya da inganci mai karfi. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp