Kungiyar masu Kananan Masana’antu ta Nijeriya (ASBON) ta bayyana cewa, fiye da kananan masana’antu miliyan 10 ne suka durkushe a shekarar da ta gabata 2023.
Shugaban kungiyar, Femi Egbesola, ya sanar da haka a tattunawarsa da manema labarai, ya ce, kamfanonin sun durkushe ne sakamakon matsalar tattalin arziki a Nijeriya.
- Kwastam Ta Tara Biliyan 52.7 A Kano Da Jigawa A 2023
- Kasashen Afirka Na Fadada Cudanya Da Kasar Sin A Fannoni Daban Daban
Janye tallafin man fetur da Shugaban Kasa Bola Tinubu ya yi a yayin rantsar da shi ranar 29 ga wata Mayu 2023 da kuma karin farashin man fetur da sauran kayan masarufi sun kara hauhawar farashin kayyakin amfanin yau da kullum wanda ya haifar da rashin aikin yi ga matasa wanda kuma ya kai ga karin talauci a tsakanin ‘yan Nijeriya.
Hukumar kididdiga ta kasa NBC ta bayyana cewa a watan Nuwamba na 2023 an samu hauhawar farashi na kashi 28.20 ba kamar yadda yake ba a watan Oktoba 2023 na kashi 27.33.
Da yake tsokaci a kan yadda matsin tattalin arzikki ya shafi mambobinsu, Egbesola ya bayyana cewa, “Kashi 25 na kamfanonin da ake da su suka mutu a shekarar 2023, wannan ne mafi yawa a tarihin mutuwar kamfanoni a kasar nan.
“A halin yanzu muna da kamfanoni miliyan 40 a kasar nan da bayanan su ke cikin kundin tattara bayanai, idan ka cire kashi 25, yana nuna kenan kamfanoni miliyan 10 suka mutu.
“A wasu kasashen in har aka samu irin haka, gwamnati na sanya dokar ta-baci ne a sashin don wadannan kanana kamfanoni sune ke rikida su zama manyan kamfanoni a nan gaba. Idan zaka kuma yi tambaya a cikin shekara 10 da suka wuce kananan kamfanoni nawa ne suka zama manyan kamfanoni? Lallai ba a abin a zo a gani ba ne”
Ya kuma kara da cewa, in har ana son ceto kananan kamfanoni daga durkushewa a cikin wannan sabuwar shekarar dole gwamnati ta tabbatar da gyara hanyoyi da kuma samar da wutar lantarki da kuma samar da bashi mara ruwa ga kananan kamfanoni don tabbatar da bunkasar su.
In har aka samar da wadannan tabbas kamfanoni da dama za su bunkasa, su kuma taimaka wajen daukar matasanmu aikin yi abin da kuma zai rage ayyuykan masu aikata laifukka a fadin tarayyar Nijeriya.