• Leadership Hausa
Thursday, March 23, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kananan Sana’oi Da Ci Gaban Kasa (3)

by Hussaini Najidda Umar
7 months ago
in Labaran Kasuwanci, Sana'a Sa'a
0
Kananan Sana’oi Da Ci Gaban Kasa (3)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Abu na gaba da zan kuma tattaunawa a nan shi ne, shin kuwa wadannan kananan sana’oin da ‘yan Nijeriya suke yi suna biya musu bukatunsu? 

A nan zan ce eh suna biya musu, sai dai kawai ba kamar yadda ake so ba.

  • Shugaba Buhari Zai Kawo Karshen Rashin Tsaro A Nijeriya -Buratai
  • Tarihi Baya Mantuwa

Musamman yanzu da abubuwa suka yi tsada saboda matasalar tashin kayyakin yau da kullum.

Wannan kuwa dalilai ne masu yawan gaske da suka jawo wannan tsadar tun da ba wai kawai Nijeriya ba ce take fama da wannan matasalar ba har da sauran kasashen duniya.

Mene ne mai karamar sana’a ya dace ya yi a irin wannan lokaci na tsadar rayuwa da tsadar kaya?

Labarai Masu Nasaba

Karancin Kudi: Mun Yi Asarar Kwai Na Biliyan 30 -Masu Kiwo

Kamfanin Siminti Na Dangote Ya Samu Gaggarumar Riba Da Bunkasa A 2022

Abin da ya kamata mai karamar sana’a ya yi a wannan lokaci su ne na daya, ya san me yake samu. Ina nufin shin kasuwancin nasa yana bashi riba ko a’a,?

A nan ina so na fada wa mai karatu cewa akwai mutane da suke sana’a kullum, amma ba su san me suke samu ba. Saboda ba sa yin lissafin riba da faduwa.

Shi ne ya sa sai ka ga dan kasuwa lokaci guda ya karye ya rasa mene ne dalili, dalilin kuwa shi ne, shi da kansa ne ya cinye duk ribar da yake samu a kasuwancinsa.

Saboda haka ya zama dole mai sana’a ya rika rubuta abin da yake samu a kullum.

Sannan kuma ya rinka sanin kullum idan ya tashi daga kasuwa me ya samu, riba ko akasin haka.

Duk dan kasuwa ba sai an fada masa yadda ya kamata ya yi lissafin ba domin ya sani.

Saboda haka abu ne mai kyau mai karamar sana’a ya san me yake samu kullum ta hake ne yake da ma’auni a hannunsa yadda kullum zai rinka auna kasuwancinsa.

Sannan abu na biyu shi ne dan kasuwa ya san inda kasuwacinsa yake so ya kai shi.

A nan ina nufin duk wani mai yin sana’a ya rubuta a takarda manufofinsa da abin da yake so ya cimma a karshe.

Misali mutum zai shiga kasuwanci ya ce yana so ya tara miliyan 10 a shekara biyu ko uku. Anan dan kasuwa shi ne zai zayyana hanyoyin da zai bi ya tara kudin.

Sannan kuma ya rinka bin duk wannan ka’idojin da manufofin da ya rubuta.

Ana so duk dan kasuwa komai kankantar jarinsa ya kasance ya na da manufa da burin inda yake so kasuwancinsa ya kai shi.

Akwai kamfanoni da yawa a kasashen duniya da suka fara da kadan-kadan amma saboda sun yi tsari mai kyau da zayyana inda kasuwancinsu suke so ya je a shekarun da mutum ya tsara za’a ga wannan kamfanin ya kai.

Har ila yau, duk dan kasuwa ya sani cewa makomar kasuwancinsa tana hannunsa, a nan shi ne mai ruwa da tsaki ko mai wuka da nama ta komai na kasuwancinsa.

Shi ne ya sa dole dan kasuwa ya yarda da kasuwancin da yake.

Saboda yawancin ‘yan kasuwa suna yin kasuwanci amma ba sa son kasuwacin a ransu, shi ne dalilin da ya sa sai mutum yaga kasuwancin nasa bai kai shi ko ina ba.

Dole ne mutum ya yarda da abin da yake kada a tambaye ka kace ‘to gamu nan dai wannan kasuwancin dai muna yinsa ne’.

Kada dan kasuwa ya rinka fadar haka saboda yana nuna bai yarda da kasuwancin ba, shima kuwa kasuwancin ba zai yarda, da shi ba.

Abu na ga ba shi ne duk mai karamar sana’a ya saka a ransa cewa wannan sana’ar ita ce rayuwarsa.

A nan ina nufin sana’arka ta zamanto maka ita ce abokiyar rayuwa, yadda idan wani abu ya same ta ya sami rayuwarka.

Ta ya ya za’a mayar da kasuwanci ya koma abokin rayuwa,?

Hanya daya ce tak, ita ce ka yarda a ranka cewa idan babu ita babu kai. In dai ka yi haka to hakika kasuwancinka zai kai ka inda kake so musamman idan ka tsara manufofin masu inganci da kuma yiwuwa.

Kada ka kirkiri abin da ba zai yiwu ba. Kada ka zauna ka rubuta ka ce kana a kwana 100 sana’arka ta tara maka Naira miliyan Dubu, idan ka yi haka to ka fara tambayar kanka nawa ne jarin da ka zuba da zai kawo maka Naira Biliyan dubu?

Wannan shi ne burin da ake cewa ba zai yiwu ba.

A koda yaushe ka gina kasuwancinka a kan gaskiya da amana, saboda wadannan abunbuwan guda biyu su ne tushen ci gaban duk wani kasuwanci da mutum ya sa a ransa zai fara.

Sannan abu na karshe mai son ya yi kasuwanci, kada ka ko ki taba shiga kasuwancin da ba ka ko ki da ilimi a kai.

Wannan shi ne babban kuskuren da mutane suke yi a yanzu na shiga kasuwancin da ba su da ilimi a kansa.

Bincike ya nuna mutane a duniyar nan tamu suna dogara ne kacokan ga kayyayyakin da masu kananan sana’oi suke samarwa.

Idan an kula anan za’a ga su irin wadannan sana’o’i ba wai kawai suna taimakawa masu su bane a’a har da mu al’umma da muke amfana daga kayayyakinsu.

Kamar yadda na fada a baya rashin yarda da sana’a shi ne babbar matsalar da take sawa mutane basa zuwa inda suke so su je ta hanyar sana’oinsu.

Saboda haka ne ya zama wajibi jama’a mu riki sana’a komai kankantarta, saboda yanzu mun fahimta wadananan kananan sana’oin su ne ginshikin ci gaban kasa.

A nan nake kira da babbar murya ga gwamnatocinmu kama daga gwamnatin tarayya, da gwamnatin jihohi da kananan hukumomi da su ci gaba da bijiro da shirye-shirye da tsare-tsare wadanda za su kuma taimaka wa ‘yan kasuwa kanana domin gabatar da sana’oinsu a cikin hali mai kyau da ci gaba.

Mun san cewa yawancin masu kananan sana’o’i musamman wadanda suke a cikin gidaje ba sa ba wa gwamnati haraji saboda ba’a san ma suna yin sana’ar ba.

Amma a lokuta da yawa a kan ga yadda masu sana’oi da suke kan tituna da ciki kasuwannni suke shan karbar kudade daga masu karbar haraji daban-daban.

A wata hira da na yi da masu sana’oi daban-daban a kan haraji sun fada min cewa harajin da suke biya yana yin yawa matuka, sannan kuma hukumomi masu karbar harajin suma yawansu na da yawa har ma dan kasuwa ya rasa gurin da zai biya harajinsa.

Misali; za’a ga masu karbar haraji daga kananan hukumomi daban, sannan masu karbar haraji daga bangaren gwamnatin jihohi suma dama.

Har ila yau ita ma gwamnatin tarayya ba’a barta a baya ba, domin za’a ga masu zuwa karbar haraji suma daga wajensu.

Ta haka ne ya kan sa ‘yan kasuwa da yawa suke korafi da neman don me gwamnati ba za ta hade harajin ya zama daya ba ta yadda idan ka biya sau daya duk wadansu hukumomi suma da suke karbar haraji za su samu kasonsu daga biya guda daya da dan kasuwa ya yi?

Hakika biyan kudin haraji wani babban al’amari ne ga gwamnatoci, kuma tabbas wadannan harajai da ake biya su ne suke tafiyar da aikin gwamnati in dai an yi abin da ya dace da kudin da aka karba.

Saboda haka ya zama dole gwmanatoci su zauna su lalubo hanyoyin da ‘yan kasuwa za su samu sauki wajen biyan kudin haraji, sannan kuma idan sun biya su gani a kasa.

Tags: Al'amuran Yau Da KullumBiyan BukatuCi Gaban KasaKasuwanciSana'o'i
ShareTweetSendShare
Previous Post

Mata A Daina Yawace-yawace Da Shige-shige Mara Amfani -Halima Kassim

Next Post

Sin Ta Sanyawa Mataimakiyar Ministan Sufurin Kasar Lithuania Takunkumi

Related

Karancin Kudi: Mun Yi Asarar Kwai Na Biliyan 30 -Masu Kiwo
Labaran Kasuwanci

Karancin Kudi: Mun Yi Asarar Kwai Na Biliyan 30 -Masu Kiwo

6 days ago
Kamfanin Siminti Na Dangote Ya Samu Gaggarumar Riba Da Bunkasa A 2022
Labaran Kasuwanci

Kamfanin Siminti Na Dangote Ya Samu Gaggarumar Riba Da Bunkasa A 2022

2 weeks ago
Yadda Ake Hada Sabulun Wanki Na Sayarwa
Sana'a Sa'a

Yadda Ake Hada Sabulun Wanki Na Sayarwa

4 weeks ago
Madubin Sauyin Kudi Daga Wasu Kasashen Duniya Masu Tasowa
Labaran Kasuwanci

Madubin Sauyin Kudi Daga Wasu Kasashen Duniya Masu Tasowa

4 weeks ago
Sana’ar Kayan Sufiri
Sana'a Sa'a

Sana’ar Kayan Sufiri

1 month ago
Ya Kimar Mace Mara Sana’a Take A Wurin Mijinta?
Sana'a Sa'a

Ya Kimar Mace Mara Sana’a Take A Wurin Mijinta?

1 month ago
Next Post
Sin Ta Sanyawa Mataimakiyar Ministan Sufurin Kasar Lithuania Takunkumi

Sin Ta Sanyawa Mataimakiyar Ministan Sufurin Kasar Lithuania Takunkumi

LABARAI MASU NASABA

Siyasantar Da Batun Gano Asalin COVID-19 Dabara Ce Ta Boye Gaskiya

Siyasantar Da Batun Gano Asalin COVID-19 Dabara Ce Ta Boye Gaskiya

March 23, 2023
Jirgin Saman Nijeriya Zai Fara Aiki Kafin Ranar 29 Ga Mayu

Jirgin Saman Nijeriya Zai Fara Aiki Kafin Ranar 29 Ga Mayu

March 23, 2023
Ina So A Ko’ina A Ji Hikima Da Fasaharmu – Yusuf King

Ina So A Ko’ina A Ji Hikima Da Fasaharmu – Yusuf King

March 23, 2023
Hadin Gwiwar Sin Da Rasha Na Da Muhimmanci Sosai Ga Duniya

Hadin Gwiwar Sin Da Rasha Na Da Muhimmanci Sosai Ga Duniya

March 23, 2023
Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumin Gobe A Wasu Birane

Ramadan: Lokutan Sahur Da Buda-baki Na Azumin Gobe A Wasu Birane

March 23, 2023
Gyare-gyare Su Kan Faru Ne Bisa Sauyawar Tunanin Mutum

Gyare-gyare Su Kan Faru Ne Bisa Sauyawar Tunanin Mutum

March 23, 2023
NLC Za Ta Shiga Yajin Aiki Saboda Karancin Kudi A Nijeriya

NLC Za Ta Shiga Yajin Aiki Saboda Karancin Kudi A Nijeriya

March 23, 2023
FEC Ta Amince Da Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Wajen Gina Barikin Jami’an NDLEA

FEC Ta Amince Da Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Wajen Gina Barikin Jami’an NDLEA

March 23, 2023
Mata Magoya Bayan PDP Na Zanga-Zangar Watsi Da Sakamakon Zaben Gwamnan Kaduna

Mata Magoya Bayan PDP Na Zanga-Zangar Watsi Da Sakamakon Zaben Gwamnan Kaduna

March 23, 2023
DSS Ce Abokiyar Hamayyar Mu A Jihar Kano Ba APC Ba – NNPP

NNPP Ta Zargi Gwamnatin Ganduje Da Kai Hare-Hare Kan Mazauna Kano

March 23, 2023
ADVERTISEMENT
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.