Kyaftin din Tottenham Hotspur Hary Kane ya zura kwallaye 4 rigis a ragar Shaktar Donetsk ta kasar Ukraine a wasan sada Zumunci da suka buga.
Kane ya shiga shekarar karshe na kwantiraginsa na shekaru shida a Spurs.
Inda Bayern Munich ke nemansa,yayin da kungiyar ta Jamus ta gabatar da tayin karshe na neman dan wasan ranar Juma’a.
Amma Spurs din sun nuna cewa Kane ba na sayarwa bane a lokacin kasuwar musayar ‘yan wasa.
Kane, mai shekaru 30, bai nuna alamar tsayawa ba yayin da ya zura kwallo a raga a cikin mintuna 55 da Shakhtar a wasan farko na sabon koci Ange Postecoglou a Tottenham Hotspur.
Magoya bayan Spurs sun yi wa kociyan Australia Postecoglou liyafar girmamawa kuma.
Inda suka dinga hayaniya da aka sanar da cewa Kane zai zama kyaftin din kungiyar ta arewacin London idan Hugo Lloris ya bar ta.
Ina sha’awar Ganin Kane a Tottenham amma kuma yana da ra’ayi na rashin kai akan zamansa ko tashinsa inji Postecoglou.