Ƙungiyar masu gwanjon kayayyaki ta Nijeriya (NAA) reshen Kano ta ce gwamnatin jihar na asarar a ƙalla Naira biliyan ɗaya duk shekara saboda rashin yin gwanjon tsoffin kayayyakin gwamnati da aka cire daga ofisoshi da wuraren gyare-gyare.
Sakataren ƙungiyar a jihar, Isah Deneji, ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a Kano, inda ya ce ana cire kayayyaki irin su kujeru, da na’urar sanyaya ɗaki, da interlock sakamakon sabuntawa, amma maimakon a yi gwanjonsu, ana barin wasu ma’aikata su sace su su sayar.
- NDLEA Ta Kama Wani Matashi Dan Shekara 29 Da Kwayoyin Tramadol 7,000 A Kano
- An Kama Matasa 2 Kan Nuna Makamai A Shafukan Sada Zumunta A Kano
Ya yi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya umarci Kwamishinan Kuɗi ya dawo da tsarin yin gwanjon kayayyakin gwamnati da aka ayyana a matsayin tsofaffi, domin hana ɓarna da satar da ake fama da shi a yanzu. Ya ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da cewa kuɗin da aka samu ya shiga asusun gwamnati ba tare da salwanta ba.
Deneji ya ƙara da cewa, akwai rahotannin da ke nuna an sace sama da na’urar sanyaya ɗaki guda 20 daga wurin gyaran gidan gwamnati. Ya kuma jaddada cewa su ƙwararru ne masu lasisi da ake sabuntawa duk shekara, amma gwamnatin jihar ta daina amfani da su.
A nasa ɓangaren, Kwamishinan aiyuka, Marwan Ahmad, ya ce ba ma’aikatarsa ce ke kula da gwanjon kayayyakin gwamnati ba, sai dai ma’aikatar kudi. Sai dai ya yi Allah-wadai da yadda jama’a ke kwasar kayayyakin gwamnati daga wuraren da ake gudanar da gyare-gyare. Ya ce a baya-bayan nan sun kwato interlock din da aka cire wanda darajarsa ta kai sama da Naira miliyan ɗaya, wanda daga bisani aka sake amfani da shi a wani wuri na gwamnati.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp