Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars da ke buga gasar Firimiyar Nijeriya, ta ƙulla yarjejeniya da RFI Hausa, wato sashen Hausa na gidan rediyon Faransa.
A wata sanarwa da suka fitar, an bayyana cewa daga wannan kakar wasa ta shekarar 2025/2026, RFI Hausa za ta zama abokiyar hulɗar Kano Pillars.
- Dele Momodu Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP Zuwa ADC
- Za A Ci Gaba Da Zaman Makokin Buhari A Abuja – Garba Shehu
Sanarwar RFI Hausa ta ce: “Kano Pillars ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Nijeriya, tana farin cikin sanar da sabuwar hulɗarta da RFI Hausa, wacce ta shahara wajen yaɗa labarai, wasanni da al’adu a cikin Nijeriya da ƙetare.”
Sabuwar hulɗar za ta gudana ne ƙarƙashin sabon manajan ƙungiyar, tsohon ɗan wasan Nijeriya, Ahmed Musa.
Wannan shi ne karon farko da RFI za ta ɗauki nauyin wata ƙungiya a ɓangaren wasanni.
Yarjejeniyar ta haɗa da:
- Ɗaukar nauyin sabbin kayan wasanni da na horo
- Samar da kayan aikin ɗaukar labarai na zamani
- Ba da horo ga ma’aikatan labarai na Kano Pillars
- Yaɗa labaran ƙungiyar a shafukan RFI Hausa
An shirya wannan yarjejeniya ne domin taimaka wa Kano Pillars ta ƙara samun ɗaukaka da ci gaba a harkar ƙwallon ƙafa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp