Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta dakatar da Kocinta Usman Abdalla, tsawon makonni uku, sakamakon rashin ƙoƙari da kuma nuna halayyar da bata kamata ba ga magoya bayan ƙungiyar.
Kungiyar ta ɗauki wannan matakin ne bayan tashi daga wasan da ta buga canjaras (0-0) da Bayelsa United a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano a ranar Lahadi 2-02-2925.
- Shin Dawowar Ahmad Musa Za Ta Taimaka Wa Kano Pillars?
- NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars N2m, Ta Dakatar Da Ɗan Wasanta
Ƙungiyar dai tana fama da rashin nasara a ƴan kwanakin nan inda a cikin wasanni uku wasa ɗaya kawai ta samu nasara.
Bayan tashi daga wasan ne magoya bayan ƙungiyar suka yi wa Usman Abdalla ihu, kamar yadda rahotanni suka bayyana, lamarin da bai yi wa mai koyarwar daɗi ba shi kuma ya mayar da martani.
Tsohon ɗan wasan ƙungiyar, Ahmad Garba Yaro-Yaro, shi ne zai ci gaba da jagoranci ƙungiyar a matsayin riƙon ƙwarya tare da taimakon Abubakar Musa da tsohon ɗan wasa Gambo Muhammad da Sulaiman Shua’aibu da kuma Ayuba Musa.
Kawo yanzu Kano Pillars, wadda take mataki na 10 da maki 29 za ta fafata da Remo Stars a wasan mako na 23.