Kungiyar kwallon kafa 6Kano Pillars ta raba gari da kocinta, Paul Offor, bayan wata guda kacal da bashi ragamar jagorancin kungiyar.
An yanke shawarar rabuwa ne bisa ga yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu, kuma hakan ya biyo bayan saukar tsohon mai horarwa, Abdul Maikaba.
- Za A Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomin Kano A Watan Nuwamba
- An Kaddamar Da Shirin “Sabon Zamani Da Sabon Fim” Karo Na 2
A wata sanarwa da Shugaban Kungiyar, Ali Muhammad Umar, ya fitar, ya bayyana cewa an yanke shawarar ne a wani mataki na yi wa kungiyar garambawul.
Offor, ya jagoranci kungiyar Sporting Lagos wajen lashe kofin Naija Super 8.
Duk da nasarorin da Offor ya samu, zamansa da Kano Pillars ya zo karshe a wani yanayi na ba-zata.
Kungiyar yanzu tana neman sabon mai horaswa da zai jagoranci tawagar a kakar gasar Firimiyar Njjeriya ta shekarar 2024/25.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp