Ƙwallon ɗaya tilo da kyaftin din ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars Ahmed Musa ya ciwa ƙungiyar tayi sanadiyar samun nasarar farko da ƙungiyar tayi tun bayan fara wannan kakar wasannin ta bana.
Pillars ta doke abokiyar karawarta Enugu Rangers da ci 1-0 a wasan da suka buga a filin wasa na Sani Abacha dake birnin Kano inda ɗaruruwan magoya bayan ƙungiyoyin biyu suka shaidi wasan.
- Kano Pillars Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Gidan Rediyon RFI Hausa
- Zan Yi Ƙoƙarin Dawo Da Martabar Kano Pillars A Idon Duniya — Ahmed Musa
Kafin yanzu ƙungiyar, mallakar gwamnatin jihar Kano ta yi rashin nasara biyu sannan ta buga canjaras ɗaya a wasanni uku da ta buga a wannan kakar, wannan nasarar da Sai Masu Gida suka samu ta sa ta koma matsayi na 17 a teburin gasar ta NPFL.
Pillars ta fara wasan na wannan mako da zimmar samun nasara bayan rashin nasarar da ta yi a hannun Katsina United a wasan Mako na 3 da suka buga a filin wasa na Muhammadu Dikko dake birnin Katsina, kyaftin Ahmed Musa wanda ya dawo daga raunin da yayi fama da shi, ya fitar wa Pillars kitse daga wuta a wasan na yau.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp