Majalisar zartarwa ta jihar Kano ta amince da fitar da fiye da Naira biliyan 8.2 don gudanar fa wasu jerin ayyuka domin ƙara haɓaka harkokin ilimi, ƙarfafa samar da ruwan sha, da kuma inganta ingancin makamashi a faɗin jihar.
An sanar da amincewar ne a cikin sanarwa daban-daban da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya fitar a ranar Lahadi, wanda ya ce an cimma matsayar ne a lokacin taron majalisar na 33 wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta.
- Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya
 - Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba
 
A cewar Bature, an ware sama da Naira biliyan 4.9 don muhimman ayyukan ilimi da nufin haɓaka ababen more rayuwa, inganta matakan koyo da faɗaɗa samun ingantaccen ilimi.
Har ila yau, majalisar ta amince da Naira biliyan 3.3 don ayyukan samar da ruwa da makamashi domin inganta samar da ruwa mai tsafta da aminci a cikin al’ummomin birane da karkara.
Daga cikin ayyukan samar da ruwan, an amince da gina tashar tace ruwa ta zamani a Taliwaiwai da ke ƙaramar hukumar Rano, da kuma biyan bashin kuɗin wutar lantarki da man fetur da ake bin hukumar ruwa ta jihar don ci gaba da ayyuka.
Wani ɓangare na kuɗaɗen zai kuma haɗa da biyan basussukan da kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) ke bi, siyan dizal (AGO) da man fetur (PMS) don ayyukan tashoshin tace ruwa, da kuma kula da kayayyakin da tashoshin ke bukata don samar da ruwa tsaftatacce.
			




							








